Daga JOHN D WADA a Lafia
Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa ta ce ta ƙara ƙaimi wajen ceto ɗalibai shida na Jami’ar Nasarawa da ke Keffi, wadanda ‘yan bindiga suka sace a Gudi, ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP Rahman Nansel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Lafia.
SP Nansel ya ce an sace ɗaliban ne a ranar 6 ga Mayu da misalin ƙarfe 9 na dare lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka farmaki wani masauki na ɗalibai da ke wajen harabar jami’a a Anguwar Ninzo, Gudi, da ke gefen garin.
A cewarsa an gano shida daga cikin waɗanda aka sace a matsayin ɗalibai na Faculty of Engineering da ke Gudi Campus na Jami’ar Nasarawa da ke Keffi yayin da wani kuma ba ɗalibi ba ne, dan baƙo ne a masaukin a lokacin da lamarin ya faru.
Kakakin ‘yan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan a jihar Shetima Mohammed Jauro ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru domin ganewa idon shi.
Ya ce kwamishinan ya sake jaddada wa ɗalibai mazauna yankin da jami’ar cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da an ceto waɗanda suka rage.
SP Nansel ya ce kwamishinan ya kuma sake tura kwamandan ‘yan sandan na shiyar Akwanga domin jagorantar ayyukan filin har sai an ceto sauran waɗanda aka sacen
Ya ƙara da cewa an tura haɗaɗɗen tawagar tsaro da ta ƙunshi ‘yan sanda, SSS, sojoji, NSCDC, ‘yan banga da sauran ƙungiyoyin dabara domin ƙara kaimi a aikin ceton.
“Aikin yana da nufin bin diddigin masu garkuwa da mutanen da ceto waɗanda aka sacen ba tare da an cutar da su ba da kuma gurfanar da masu laifin a gaban kuliya daga bisani” in ji shi.
Daganan sai kakakin ‘yan sandan ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu su kasance a faɗake kuma su kula da tsaron kansu sannan ya roƙi duk wanda ke da bayanin da zai taimaka ya kai shi ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wasu hukumomin tsaro.
Ya ƙara da cewa za a ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da ya taso yayin da bincike da aikin ceto ke gudana.
