El-Rufa’i ya janye ƙorafe-ƙorafe uku bayan ba kotu haƙuri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Lauya mai kare tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Paul Erokoro (SAN), ya ba wa Babbar Kotun Jihar Kaduna haƙuri da kuma neman janye buƙatu guda uku da lauyoyin El-Rufa’i suka shigar a shari’ar rashawa da ake yi akansa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Erokoro, wanda a kwanan ya zama mai kare El-Rufai, ya kuma ce ya shirya sabon ƙorafi da zai gabatar wa Mai Shari’a Darius Khobo nan da wani ɗan lokaci.

Hakan na zuwa ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta zargi lauyoyin tsohon gwamnan da jinkirta fara sauraren shari’ar ta gabatar da sababbin ƙorafe-ƙorafe duk da cewa masu ƙara sun ce a shirye suke a cigaba da shari’ar.

Yayin da aka gabatar da shari’ar Erokoro ya ce buƙatun da lauyoyin El-Rufa’i na baya suka gabatar, an janye su. Don haka ne ya ba wa kotun haƙuri bisa cewa bai amince da wasu lafuzza ba acikin ƙorafe-ƙorafen a madadin El-Rufa’i.

Ya bayyana cewa, bayan karɓar ragamar kare tsohon gwamnan, ya yi nazari akansu, lamarin da ya sa ya ga dacewar gabatar da sabuwar buƙata da soke na bayan.

Sannan, ya nemi kotun da ta dakatar da hukunci akansu tare da neman a ƙara masa lokaci domin shigarwa da kuma kimtsa wa zama na gaba akan shari’ar a tsanake.

By Babaji

Leave a Reply