Gwamnatin Kano ta biya bashin kuɗin magunguna biliyan N1.2 da ta gada — Pharm. Ghali Sule

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Daraktan Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Lafiya ta Jihar Kano (DMCSA), Pharm. Ghali Sule, ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta biya bashin magunguna da ta gada daga gwamnatin da ta gabata wanda ya kai Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari biyu.

Pharm. Ghali Sule ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar hukumar a Kano, a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru uku na gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce an shirya bikin na tsawon mako guda domin nuna nasarorin da gwamnatin ta samu a fannin lafiya, musamman ta fuskar samar da ingantattun magunguna da kayan aikin lafiya a asibitocin gwamnati.

A cewarsa, biyan bashin da aka gada ya taimaka matuƙa wajen dawo da amincewar kamfanonin samar da magunguna da kuma tabbatar da wadatar magunguna a asibitocin jihar.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan bashin magunguna da ya kai Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari biyu ga kamfanonin samar da magunguna, lamarin da ya taimaka wajen dawo da wadatar magunguna a asibitocin jihar,” inji shi.

Ya ƙara da cewa kafin biyan bashin, wasu daga cikin kamfanonin sun fuskanci matsalolin kuɗi har ma wasu suka fara durƙushewa sakamakon rashin biyan kuɗaɗensu.

Pharm. Ghali Sule ya kuma bayyana cewa daga cikin nasarorin da aka samu akwai gina katafaren ɗakin ajiyar magunguna mallakar hukumar, wanda a baya babu irinsa a jihar.

Ya ce a da duk lokacin da gwamnatin tarayya ta aiko da tallafin magunguna, sai an kai su jihar Sokoto domin ajiya kafin daga bisani a dawo da su Kano, abin da ke haddasa ƙarin kashe kuɗaɗe da wahalhalu.

Ya bayyana cewa ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai ƙaddamar da sabon ɗakin ajiyar magungunan a cikin makon bikin.

Daraktan Janar ɗin ya ce daga cikin abubuwan da za su gudana a yayin bikin akwai addu’o’in neman zaman lafiya da nasarar ƙasa, laccoci kan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da kuma taron wayar da kan jama’a tare da haɗin gwiwar hukumomin NAFDAC, NDLEA da likitocin asibitocin kula da masu fama da matsalolin kwakwalwa.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar masu kamfanonin samar da magunguna za ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin gudunmawar da gwamnatinsa ke bayarwa wajen inganta harkokin lafiya a jihar.

Pharm. Ghali Sule ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar cikakken goyon baya da haɗin kai domin ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar jama’a.

By ukarofi

Leave a Reply