Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Makarantar Amina Dala Comprehensive College da ke ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano ta karrama wasu fitattun mutane bisa gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa al’umma da kuma bunƙasa harkokin ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci a jihar.
An gudanar da bikin karramawar ne a yayin saukar karatun Alƙur’ani mai girma na mahaddata 15 da aka shirya a dakin taro na Cibiyar Koyar da Ilimin Siyasa da ke Mambayya a Kano a makon da ya gabata.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maiduguri, Dr. Adamu Yunusa Dangwani, Gwaggo Fatsama Dantata, Dr. Salisu Sambajo, Alhaji Sani Isa, shugaban rukunin kamfanonin Asia, Alhaji Munzali Muzab, Hon. Muhammad Kasim Umar Warure da sauran fitattun mutane.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Daraktan makarantar, Malam Sunusi Ibrahim Kulita, ya bayyana cewa an karrama mutanen ne saboda irin gudummawar da suke bayarwa wajen taimaka wa al’umma da kuma tallafa wa harkokin ilimi da ci gaban makarantar.
Ya kuma taya ɗaliban da suka haddace Alƙur’ani murnar wannan nasara tare da kira gare su da su kasance masu aiki da koyarwar Alƙur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum.
Haka kuma ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafa wa marasa galihu da kuma harkokin ilimi.
A nasa jawabin, Dr. Adamu Yunusa Dangwani ya taya mahaddatan murnar saukar Alƙur’ani tare da sanar da bayar da tallafin kuɗi na Naira dubu ɗari biyar ga makarantar.
Ya bayyana jin daɗinsa bisa lambar yabon da aka ba shi, yana mai cewa wannan karramawa za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan alheri da tallafa wa harkokin ilimi da ci gaban al’umma.
