Rashin tsaro ya janyo ƙarancin zuma a Nijeriya – Aminu Musa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban wani kamfanin samar da zuma da sarrafa kayayyakinta a Nijeriya, Alhaji Aminu Musa Kofar Kwari Madurasa, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta janyo raguwar samar da zuma a Nijeriya duk da irin yalwar dazuzzuka da ƙasar ke da su.

Ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a Kano, inda ya ce Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke samar da ingantacciyar zuma mai yawa a duniya.

A cewarsa, matsalolin tsaro sun hana masu sana’ar tattara zuma shiga dazuzzuka domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya ce zuma na taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar jama’a da bunƙasa tattalin arziki, lamarin da ya sa ya zama wajibi gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin tsaro.

Alhaji Aminu Musa ya kuma bayyana hanyoyin da ake gane ingantacciyar zuma, inda ya ce masana na iya gane ta ta hanyar launi da kauri, yayin da talakawa za su iya amfani da wasu hanyoyi na gargajiya wajen tantance ingancinta.

Ya kuma yaba wa ƙungiyar ‘yan kasuwa ta KASCOTE ƙarƙashin jagorancin Alhaji Hassan Yaro bisa ƙoƙarinta na bunƙasa harkokin kasuwanci ta hanyar shirya taruka da haɗa kamfanoni daga Nijeriya da ƙasashen waje.

By ukarofi

Leave a Reply