Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumomin lafiya a Nijeriya sun bayyana damuwa kan ci gaba da yaɗuwar zazzaɓin Lassa bayan da cutar ta yi sanadin mutuwar mutum 221 a watanni shida na farkon shekarar nan.
Alƙaluman da cibiyar dakile da yaƙi da cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta fitar sun nuna cewa an tabbatar da cutar ta kama mutum 922 a watan Yuni.
Bayanan sun kuma nuna cewa kaso 24 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar sun mutu, sama da kaso 18.7 da aka samu a daidai wannan lokaci a bara.
Jami’an lafiya sun ce sabbin waɗanda suka kamu da cutar sun ƙaru a makonni uku a jere.
“Daga mutum 13 da aka tabbatar sun kamu a mako na 24, adadin ya karu zuwa 22 a mako na 25, sannan ya kai 31 a mako na 26,” inji sanarwar.
NCDC ta ce cutar ta fi bazuwa a jihohi 23 daga cikin jihohi 36 na Nijeriya, inda jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benue da Edo ke kan gaba wajen masu ɗauke da cutar, inda suke da kusan kashi 85 na waɗanda suka kamu da ita a bana.
Binciken ya kuma nuna cewa matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 su ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da ma’aikatan lafiya ke ci gaba da fuskantar haɗari bayan an samu wasu sabbin kamuwa a tsakaninsu a makonnin baya-bayan nan.
Zazzaɓin Lassa cuta ce da ke haddasa zubar jini, kuma tana yaɗuwa ne galibi ta hanyar abinci ko kayan gida da suka gurɓace da fitsari ko kashin wasu nau’in beraye da ke ɗauke da ƙwayar cutar.
Haka kuma cutar na iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, musamman a cibiyoyin lafiya idan ba a ɗauki matakan kariya yadda ya kamata ba.
