Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sanata Rufa’i Sani Hanga, wanda shi ne kaɗai Sanatan NDC daga Jihar Kano, a gidansa da ke Abuja a daren ranar Laraba.
Rahotanni sun ce, a cewar mai taimaka wa Sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Umar Saminu Mai-Adashi, ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna, inda ɓangarorin biyu suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi siyasar Nijeriya da ci gaban ƙasa.
Mai-Adashi ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa tattaunawar ta fi karkata ne kan yadda za a ƙarfafa dimokuraɗiyya, da inganta harkokin siyasa, tare da nemo hanyoyin bunƙasa ci gaban ƙasa.
Ziyarar dai ta ƙara ɗora zargi da hasashen cewa Sanata Hanga na dab da sauya sheƙa zuwa APC, musamman ganin yadda ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake tafiyar da al’amura a cikin jam’iyyar NDC.
A kwanakin baya, Hanga, wanda ya kasance na hannun damar tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da kasancewa fitaccen jigo a tafiyar Kwankwasiyya, ya koka kan abin da ya kira rashin adalci da aka yi masa a cikin jam’iyyar.
Sanatan ya ce an cire sunansa daga jerin ‘yan takarar da aka cimma matsaya a kansu, lamarin da ya hana shi damar sake tsayawa takarar kujerar Sanata.
Bayan wannan rikici, shugabannin APC sun ƙara zafafa yunƙurin jawo Hanga zuwa jam’iyyarsu, suna masu zargin cewa an ci amanarsa duk da irin gudunmawar da ya bayar wajen gina tafiyar siyasar Kwankwaso tsawon shekaru.
Tun a ranar Talata ma, wata babbar tawagar APC ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban APC na Jihar Kano, Salisu Maje Ahmad Gwangwazo, ta kai masa ziyara domin tattaunawa kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar mai mulki.
Ko da yake APC ba ta yi masa alƙawarin tikitin takarar Sanata ba, jam’iyyar ta tabbatar masa da cewa zai samu adalci da mutunci idan ya yanke shawarar shiga cikinta.
Rahotanni sun kuma nuna cewa APC na ƙoƙarin ƙarfafa tasirinta a siyasar Kano bayan sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar, matakin da Sanata Hanga ya yaba da shi a bainar jama’a.
Duk da cewa Hanga bai fito fili ya sanar da ficewarsa daga NDC ba, masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa ganawarsa da Shugaban APC na ƙasa wata babbar alama ce da ke nuna yiwuwar sauya sheƙarsa nan gaba.
A halin yanzu, an riga an bai wa Nasiru Yusuf Gawuna tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya da Hanga ke riƙe da ita, yayin da kuma ake cewa kujerar mataimakin gwamna da ake hasashen za a ba Hanga ta koma hannun Mustapha Rabi’u Kwankwaso, ɗan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Yayin da makomar siyasar Sanata Hanga ke ci gaba da ɗaukar hankali, masu ruwa da tsaki na ci gaba da sanya ido kan yadda sabon sauyin siyasar Kano zai kasance.
