An fara bincike kan gawar jami’ar lafiyar da ta rasu a gidan Ministan Ayyuka

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi ta fara cikakken bincike kan mutuwar jami’ar lafiya, Mary Habila, wadda ta rasu a cikin yanayi mai cike da ruɗani a harabar gidan Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, da ke garin Uburu a ƙaramar Hukumar Ohaozara ta jihar.

Marigayiyar na daga cikin tawagar likitoci da ma’aikatan lafiya da suka raka ministan zuwa garinsu lokacin da lamarin ya faru a ranar 27 ga watan Yunin 2026.

Sai dai binciken ya fuskanci tsaiko bayan da iyalan marigayiyar suka nuna adawarsu ga shirin gudanar da gwajin gawa (autopsy), duk da cewa jami’an tsaro sun bayyana hakan a matsayin muhimmin mataki domin gano ainihin musabbabin mutuwar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Joshua Ukandu, ya fitar a daren Laraba, ya ce saboda muhimmancin lamarin da kuma inda mutuwar ta faru, rundunar ta ga ya zama dole a gudanar da gwajin gawa domin tabbatar da ainihin abin da ya jawo rasuwar.

Ya bayyana cewa iyalan marigayiyar sun sanar da rundunar a hukumance cewa ba sa son a yi wa ’yarsu gwajin gawa.

Duk da haka, rundunar ta ce tana ci gaba da shirye-shiryen tuntuɓar ƙwararrun likitocin binciken gawa domin gudanar da aikin, inda ta ƙara da cewa ana jiran zuwan iyalan marigayiyar ko wakilansu saboda kasancewarsu wajibi a bisa doka kafin a gudanar da gwajin.

A cewar kakakin rundunar, jami’in kula da yankin Ohaozara ya samu kiran gaggawa kan wata matsalar lafiya da ta shafi Habila, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka garzaya zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta David Umahi (DUFUTH) da ke Uburu.

Ya ce da isar jami’an asibitin sun tabbatar musu cewa an kawo Mary Habila ne a mace.

Daga bisani, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya bayar da umarnin miƙa binciken zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.

Rundunar ta ce tuni jami’anta suka ziyarci wurin da lamarin ya faru tare da karɓar bayanai daga shaidu da sauran mutanen da ake ganin za su taimaka wajen binciken.

SP Ukandu ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta gudanar da bincike cikin gaskiya, adalci da nuna son kai ba tare da yin la’akari da matsayin kowa ba.

A gefe guda, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano haƙiƙanin abin da ya jawo rasuwar jami’ar lafiyar.

Ta hannun lauyansa, ministan ya rubuta wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ebonyi takarda yana neman a gudanar da gwajin gawa kafin a ba da gawar domin binne ta.

Umahi ya bayyana cewa gudanar da binciken kimiyya da gwajin gawa ne kaɗai zai iya kawar da jita-jita, gano gaskiya da kuma tabbatar da adalci ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

A cikin takardar da lauyansa ya aikewa rundunar ’yan sanda mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Yuli, 2026, ministan ya ce: “Dangane da yanayin da mutuwar marigayiyar ta faru, kuma domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma ingantaccen gudanar da shari’ar laifuka, muna roƙon rundunar ’yan sanda ta tabbatar an gudanar da cikakken gwajin gawa ta hannun ƙwararrun likitocin binciken gawa domin gano ainihin dalilin da ya jawo mutuwar.”

Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen kare martabar binciken da ake yi, kawar da zato da kuma tabbatar da cewa an gano gaskiyar lamarin kafin a yi jana’izar marigayiyar.

By ukarofi

Leave a Reply