Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da rabon magunguna da kayan aikin lafiya kyauta da aka bayar ta hannun Project CURE ga asibitocin jihar.
A jawabin sa a wajen bukin ƙaddamarwar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa wannan wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa tsarin kiwon lafiya ta hanyar haɗin gwiwa da abokan hulɗa da kuma ci gaba da zuba jari a fannin lafiya.
Gwamna Raɗɗa ya ce magunguna da kayan aikin da aka bayar za su inganta ayyukan asibitoci, su ƙara ƙarfafa ƙarfinsu, tare da bai wa ma’aikatan lafiya kayan aikin da suke buƙata domin samar da ingantaccen kulawar lafiya.
Ya ce, “Abin da muke ƙaddamarwa a yau wata muhimmiyar alama ce ta jajircewar gwamnatinmu wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiya da kuma tabbatar da cewa al’ummarmu sun samu ingantaccen kulawar lafiya.
Haka kuma acewar sa, yana nuna irin kyakkyawar haɗin gwiwar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da Project CURE wajen ceto rayuka da inganta lafiyar jama’a.”
A cewarsa, wannan tallafi zai rage wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi nauyin kuɗaɗen jinya da magani.
Ya ƙara da cewa, “Gwamnatinmu ta yi imani cewa kowane ɗan ƙasa ya cancanci samun ingantaccen kulawar lafiya ba tare da la’akari da halin kuɗinsa ko inda yake zaune ba. Wannan ne ke ci gaba da jagorantar dukkan jarin da muke zubawa a fannin lafiya.”
Malam Dikko ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙara kasafin kuɗin Shirin Magani Kyauta (Free Medicare Programme) da kashi 207%, lamarin da ya bai wa ƙarin al’ummar jihar damar cin gajiyar shirin.
Ya kuma bayyana wasu sauye-sauye da ake aiwatarwa domin ƙarfafa hukumar samar da magunguna da kayan aikin lafiya ta Jihar Katsina (DMSA), ciki har da kammala layin samar da magunguna, ƙara motocin jigilar magunguna, da kuma fara aiwatar da Drug Revolving Fund Programme a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 361 da aka inganta a faɗin jihar.
Ya kuma bayyana cewa an amince da ɗaukar ƙarin ma’aikata domin ƙarfafa ɓangarorin ajiyar magunguna, samar da magunguna, tabbatar da inganci, jigilar kayayyaki da kuma kula da adana kayayyaki.
“Waɗannan matakai suna cikin manyan gyare-gyaren da muke yi a fannin lafiya domin inganta kayayyakin more rayuwa, ƙarfafa tsarin samar da magunguna, da tabbatar da cewa jarin gwamnati yana haifar da ingantacciyar kulawar lafiya ga al’ummarmu.”Inji Dikko Raɗɗa.
Gwamnan ya yabawa Project CURE bisa ci gaba da haɗin gwiwa da jihar, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa zai yi tasiri mai ɗorewa ga rayuwar al’ummar Katsina.
Ya kuma buƙaci dukkan asibitocin da suka amfana da kayan aikin da magungunan da su tabbatar an kula da su yadda ya kamata tare da amfani da su bisa manufar da aka tanade su.
“Gwamnati za ta ci gaba da sa ido kan yadda ake rabawa da amfani da waɗannan kayayyaki domin tabbatar da cewa dukiyar jama’a tana amfanar mutanen da aka tanade ta domin su,” in ji shi.
Tun da farko, babbar sakatariyar hukumar samar da magunguna da kayan aikin lafiya ta Jihar Katsina (DMSA), Pharm. Fatima Shuaibu, ta ce hukumar ta samu gagarumin ci gaba tun bayan fara sauye-sauyen da gwamnatin yanzu ta kawo a fannin lafiya a shekarar 2023.
Ta bayyana cewa yawan ma’aikatan hukumar ya ƙaru daga 34 zuwa 70, yayin da Drug Revolving Fund ya ƙaru da kashi 400%. Haka kuma adadin cibiyoyin lafiya da hukumar ke kula da su ya tashi da kashi 900%, daga cibiyoyi 50 zuwa kusan 200 a faɗin jihar.
