Mahaifiyar Rotimi Amaechi ta rasu bayan shafe shekaru 89 a duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mahaifiyar abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, Mary Amaechi ta rasu bayan shafe shekaru 89 a duniya.

Ofishin yaɗa labaran Rotimi Amaechi ne ya sanar da haka a ranar Alhamis cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Mary Amaechi ta rasu ne a Alhamis bayan tsawon lokaci tana ƙoƙarin samar da son juna, haɗin kai da hidima ga al’ummarta.

Sanarwar ta kuma bayyana marigayiyar a matsayin mai riƙo da addini kuma ɗaya daga cikin fitattun matan yankinsu a lokacinta.

Haka kuma ofishin ya yaba wa al’umma akan jajentawa da tausayawa da suka nuna bisa babban rashin da ya samu tsohon gwamnan na Ribas da makusantansa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, za a sanar da lokacin da za a yi mata jana’iza a sadda ya dace.

By Babaji

Leave a Reply