’Yan sandan jihohi: An makara wajen sukar shirin – Sulaiman Abba

Spread the love

*Tsohon Sufeto Janar ya ce, amma Legas ce kaɗai yake da tabbacin shirya

*Har ’yan sandan ƙananan hukumomi ma Nijeriya tana buƙata, inji shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Suleiman Abba, ya bayyana cewa, a cikin jihohin Nijeriya bakiɗaya, Jihar Legas ce kaɗai yake da tabbacin ta shirya riƙe rundunar ’yan sandan jiha, sai dai ya ƙara da cewa, lokaci ya ƙure da za a ci gaba da bayyana wani ra’ayi na daban kan samar da rundunonin ’yan sandan jihohi a ƙasar, illa dai kawai masu ruwa da tsaki su taimaka wajen ganin shirin ya samu nasara mai ɗorewa, domin an riga an yi nisa a matakin samarwa. Don haka yana mai ra’ayin cewa, ba wai a mataki na jihohi ba, Nijeriya ta ma fi buƙatar ’yan sandan ƙananan hukumomi, saboda sun fi kusa da al’umma.

Abba, wanda shi ne Sufeto Janar na 17 na rundunar ’yan sandan Nijeriya, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News jiya Alhamis. Ya ce, Nijeriya ta wuce matakin muhawara kan ko ya kamata a kafa ’yan sandan jihohi ko a’a, inda ya jaddada cewa abin da ya rage yanzu shine a haɗa kai domin tabbatar da nasarar aiwatar da tsarin. A cewarsa, kafa ’yan sandan jihohi wani babban ci gaba ne da ke buƙatar gudunmawar kowa, domin ganin ya yi nasara.

“Mun wuce matakin bayyana ra’ayoyi kan batun ’yan sandan jihohi. Yanzu abin da ya kamata shine mu mara wa gwamnati baya, domin tabbatar da kafa tsarin yadda ya kamata, saboda cimma burin da aka daɗe ana fata,” inji shi.

Tsohon shugaban rundunar ’yan sandan ya bayyana cewa, manufar kafa ’yan sandan jihohi ita ce samar da cikakken tsarin tsaron al’umma, inda jama’a za su kasance suna taka muhimmiyar rawa wajen hana aikata laifuffuka. Ya ce, tsarin tsaron al’umma yana ba wa jama’a damar bayyana irin yadda suke son a kula da tsaronsu, wanda hakan zai ƙara haɗin gwiwa tsakanin jama’a da jami’an tsaro.

Sai dai Abba ya bayyana cewa, tun kafin batun ’yan sandan jihohi ya samu karɓuwa, shi ya daɗe yana goyon bayan kafa ’yan sandan ƙananan hukumomi. Ya ce, tun a shekarar 2009, lokacin da yake gudanar da bincike a Cibiyar Nazarin Manyan Manufofi da Dabarun ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jos, ya ba gwamnati shawarar sake kafa ’yan sandan ƙananan hukumomi, wanda aka yi a Jamhuriya ta Farko a lokacin tsarin NA. A cewarsa, wannan mataki ne da zai fi sauƙaƙa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin da suke yi wa aiki.

Sai dai ya nuna damuwa kan ko dukkan jihohin ƙasar za su iya samar da isassun kuɗaɗe domin tafiyar da rundunonin nasu yadda ya kamata. Ya ce, idan Gwamnatin Tarayya ta fuskanci ƙalubale wajen samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan ’yan sanda, akwai buƙatar a tambayi ko gwamnatocin jihohi za su iya samar da kayan aiki, horaswa da kulawar da ake buƙata.

Abba ya bayyana cewa, aikin ’yan sanda yana buƙatar kuɗi mai yawa, saboda haka ya bayar da shawarar kowace jiha ta kafa Asusun Tallafa wa Tsaro ko Asusun Tallafa wa ’Yan Sanda, domin samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan rundunar jihar.

Ya tuno da cewa, a shekara ta 2011 yayin gudanar da Babban Zaɓen ƙasa ya je Jihar Legas, inda a nan ne ya tabbatar da cewa, ita kaɗai ce jihar da ta shirya wa ɗaukar nauyin ’yan sandan jihohi, saboda tun a lokacin ta samar da isassun na’urori da ɗakunan bincike da kayan aiki isassu ga ’yan sandan Nijeriya, yana mai cewa, jihar tana ɗaukar nauyin kimanin kashi 80 cikin ɗari na motocin rundunar.

A yayin da yake magana kan tsarin da ake son aiwatarwa a matsayinsa kuma na lauya, IGP Sulaiman Abba ya bayyana cewa, gwamnatocin jihohi ne za su ɗauki nauyin kafa da gudanar da rundunonin ’yan sandansu, yayin da rundunar ’yan sandan tarayya za ta ci gaba da kula da harkokin tsaron ƙasa da manyan laifuffuka na tarayya. Ya kuma bayyana cewa, ƙudirin dokar ya fayyace nauyin da zai rataya a wuyan rundunar tarayya da ta jihohi.

A cewarsa, rundunar tarayya za ta mayar da hankali kan aiwatar da dokokin tarayya, kare muhimman cibiyoyin gwamnati da kuma yaƙi da manyan laifuffuka irin su ta’addanci da fashi da makami, yayin da rundunar jiha za ta kula da ayyukan tsaro na yau da kullum da binciken laifuffuka a cikin iyakokinta.

Haka zalika, ya jaddada muhimmancin samar da ƙa’idoji iri ɗaya a faɗin ƙasa kan jin daɗin jami’an tsaro, tsarin kuɗaɗe da haɗin gwiwa da al’umma, tare da bai wa jihohi damar tsara ayyukansu bisa ga yanayin al’ada da matsalolin tsaro da suka keɓanta da yankunansu.

By ukarofi

Leave a Reply