‎Tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Suleiman Abba ya koma PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‎Tsohon Sufeto-Janar na Rundunar ‘Yan Sanda, Suleiman Abba, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa jam’iyyar adawa ta PDP.

‎Abba ya sanar da sauya sheƙarsa ne a wani taron siyasa da aka gudanar a Bamaina da ke Jihar Jigawa, inda tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, da shugabannin PDP suka tarbe shi tare da magoya bayansa.

‎Ya bayyana cewa, ya ɗauki matakin koma wa PDP ne domin neman kujerar Sanatan mazaɓar Jigawa ta Kudu maso Yamma a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa jam’iyyar ce yake ganin za ta ba shi damar wakiltar al’ummar yankin yadda ya dace.

‎Da yake jawabi, Sule Lamiɗo ya bayyana shigar Abba cikin PDP a matsayin wani babban ci-gaba ga jam’iyyar, yana mai cewa hakan zai ƙara mata ƙarfi yayin shirin tunkarar 2027.

By Babaji

Leave a Reply