
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawa ta tabbatar da Abayomi Sunday Fasina a matsayin jakadan Gwamnatin Tarayya baƙo a fannin jakadanci duk da nuna rashin amincewa daga ɓangaren wasu ‘ya’yanta da zanga-zanga daga ƙungiyoyin al’umma kan bayar da sunanansa.
An tabbatar da shi ne bayan nazari akan rahoto da amincewar kwamitin majalisar akan harkokin waje ƙarƙashin jagorancin Sanata Sani Bello.
Da yake gabatar ta rahoton kwamitin, Sanata Simon Lalong, (APC, Jihar Filato), ya yi kira ga shugabancin majalisar da ya amince da naɗin Fasina a matsayin jakadan kuma babban kwamishina bisa la’akari da bayanan da aka samu a rahoton.
Wannan mataki ya haifar da tafka muhawara acikin sanatocin, inda wasu ciki har da Sanata Adams Oshiomhole suka nuna ƙin amincewarsu da babbar murya yayin da wasu kuma suka goyi baya.
Daga cikin waɗanda suka nuna rashin gamsuwa akwai Sanata Cyril Fasuyi daga Jihar Ekiti (APC), wanda shi ma mamba ne a kwamitin harkokin wajen.
Saidai, Shugaban majalisar, Godswill Akpabio da Sanata Abdul Ningi sun amince da shawarar kwamitin, inda suka ce ya dace Majalisar Dattawa ta yi biyayya ga sakamakon binciken hukumomi masu ruwa da tsaki akan al’amarin, wanda ya wanke shi daga tuhumar rashin cancanta da aka gabatar akansa.
