Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da biyan Naira Miliyan 500 a matsayin diyya ga mutanen da aka karɓi filayensu, gidajensu,da gonakinsu da bishiyoyisu domin aiwatar da gina gidajen Gwamnatin Tarayya na Modoji/Bakuru a Jihar Katsina.
Amincewar ya biyo bayan zaman majalisar zartarwa ta Jihar Katsina (SEC) na shekarar 2026, wanda ya gudana a babban ɗakin taro na General Muhammadu Buhari House, Gidan Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron, kwamishinan ma’aikatar filaye da tsare-tsaren birane, Dakta Faisal Kaita, ya bayyana cewa diyya za ta shafi gine-ginen da aka kammala da waɗanda ba a kammala ba, gonaki da kuma bishiyoyin waɗanda gwamnati ta karɓa domin gudanar aikin.
Kaita ya ce biyan diyyar ya yi daidai da manufar gwamnatin Dikko Raɗɗa ta tabbatar da adalci, bin ƙa’idoji da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba cikin tsari.
“Wannan amincewa ta sake nuna jajircewar mai girma gwamna wajen tabbatar da cewa duk wanda aikin ya shafa ya samu haƙƙinsa, domin tabbatar da aiwatar da manyan ayyukan gidaje da ci gaban tattalin arziki cikin lokaci,” in ji Dakta Kaita.
Ya ƙara da cewa, bayan amincewar biyan diyyar ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta mallaki sama da hektare 780 na filaye domin aikin Gidajen Gwamnatin Tarayya.
Haka kuma, majalisar ta amince da ware fili domin kafa cibiyar sarrafa kayan noma (Agro-Processing Zone) a Tashar Bala, wani shiri da ake sa ran zai bunƙasa masana’antun noma, ƙara darajar amfanin gona da samar da guraben ayyukan yi.
Majalisar ta kuma amince da tsarin kasafin kuɗi na matsakaicin lokaci (MTEF) na shekarun 2026–2027, wanda zai zama ginshiƙin tsara kasafin kuɗin jihar da manufofin kuɗi.
Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Hon. Malik Anas, ya bayyana cewa tsarin zai ƙarfafa bin ƙa’idojin kashe kuɗi, inganta rabon albarkatu, ƙara gaskiya da tabbatar da daidaiton manufofi tsakanin ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati.
“MTEF zai inganta hasashen kasafin kuɗi, daidaita tsare-tsaren sassa daban-daban da kuma ƙarfafa tsarin tsara kasafi bisa sahihan bayanan tattalin arziki.”Inji Anas
Domin ƙara bunƙasa yankunan karkara, majalisar ta kuma amince da gina Semi-Bridge a hanyar Ruma–Daneji da ke ƙaramar hukumar Sandamu, ta hanyar haɗin gwiwar gwamnatin jihar da asusun haɗin gwiwa na jiha da ƙananan hukumomi.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, Hon. Bashir Tanimu, ya ce gadar za ta sauƙaƙa zirga-zirga, inganta safarar mutane da kayayyaki tare da bunƙasa harkokin noma da kasuwanci a yankin.
A wani yunƙuri na ƙarfafa tsaro daga matakin al’umma, majalisar ta kuma amince da kafa tsarin gudanar da tarukan tsaro na kowane wata tare da shugabannin gargajiya daga matakan unguwa, ƙauye, gunduma, ƙaramar hukuma har zuwa matakin jiha.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan ƙananan hukumomi da sashen bincike, Hon. Lawal Rufai Safana, ya ce tarukan za su samar da ingantaccen dandali na tattara bayanan sirri, gaggauta kai rahoton matsalolin tsaro da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin al’umma, masarautu, hukumomin tsaro da gwamnati.
Majalisar ta bayyana cewa shawarwarin da aka cimma a zama na 11 sun sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa na gudanar da mulki cikin nagarta, bunƙasa ababen more rayuwa, ƙarfafa tsaro da tabbatar da ci gaba mai amfani ga kowa domin gina Jihar Katsina mai aminci da wadata.
