Karatun littafi tamkar makaranta yake – Jibrin Yusuf Kaila

Spread the love

“Da ina ƙarami saboda son karance-karance ake kira na da Zane Takardu Uban ‘Yan Boko”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Sunan Jibrin Yusuf Kaila ba ɓoyayyen suna ba ne, musamman ga marubuta masu mu’amala da kafafen sada zumunta. Matashi ne mai tsananin shauƙin son karance-karance da rubuce-rubuce. Yana kuma yawan rubutu kan tambihi game da harkokin rubutu da ƙalubalen marubuta. Ya fito ne daga ƙaramar Hukumar Haɗejiya ta Jihar Jigawa. A wannan makon wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya tattauna da shi game da gudunmawar sa a harkar adabi da kuma shawarwarinsa ga matasan marubuta ýan’uwan sa. A yi karatu lafiya.

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka, da harkokin da ka ke gudanarwa.

JIBRIN KAILA: Sunana Jibrin Yusuf Kaila. Ni marubuci ne, ma’akacin gwamnati, kuma ɗan kasuwa. 

Ka ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarka.

An haife ni a garin Hadejiya da ke Jihar Jigawa, a shekarar 1994 wanda ya yi daidai shekarar Musulunci 1414 Bayan Hijira. Na fara da karatu a makarantar rainon yara, zuwa firamare a rukunin makarantun Usman Bin Affan duk a garin Haɗejiya. Daga nan na tafi ƙaramar sakandire dake  Aujara. Sannan na kammala karatun sakandire a babbar sakandire ta kimiyya dake garin Kafin Hausa a shekarar 2014. Bayan kammala karatun sakandire, na shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Jigawa wacce ke garin Dutse, inda na samu shaidar kammala karatun Diploma a shekarar 2017. Haka kuma, na ƙara tafiya makarantar share fagen shiga jami’a ta School of Remedial Studies wacce ake kira da IJAMB a Jihar Katsina, a ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, na kammala a shekarar 2018. Daga nan ban cigaba da karatuna ba tukunna.

Ba mu labarin abin da ya ja hankalinka ga karance-karance.

Tun ina yaro na taso da son karance-karance. Tun a lokacin da nake aji 4 na makarantar firamare, da na lura na fara koyon haɗa baƙaƙen haruffan Hausa na A I O U E sai na ji kaunar son karatu da rubutu ya fara kama ni. Daga sannan duk abinda na gani sai na ji ina son in karanta. Har a lokacin wata ƙanwar babata ta sa min suna Zane Takardu Uban ‘Yan Boko. Kullum a gida ana ƙorafi ina tara takardu, kowacce takarda na gani sai na ɗauko ta na kawo ta gida, idan an zo shara sai an tambayi na waye? Sai ka ji ana cewa na Zane Takardu Uban ‘Yan Boko ne. A lokacin har zane ina yi, kuma babana yana saya min kala da takarda don in yi zanen da nake so. Lokacin da na fara girma kuma, sai na fara son na koyi Turanci, don haka komai na gani an rubuta da turanci sai na yi ta kokawar karantawa. Hakan ta sa ko a hanya na ga takarda musamman jarida ta Turanci, sai na ɗauka na kai gida ina gwada karantawa. Duk lokacin da aka ga ina gwagwagwa da karatun sai a yi ta min dariya, har wasu suna kirana da Philosopher, wato masanin falsafa. Ni kuma abin ba ya damu na, haka na cigaba da kwaɓa turancina, idan an samu wani mai son karatu da ya fahimci abin da nake yi sai ka ga ana gyara min. A hankali kuma har na fara zuwa laburaren Hadejiya ina karatun jarida ko littafi. Abin da na fi mayar da hankali kuwa shi ne karatun jaridun Hausa, musamman jaridar Aminiya ta mako-mako, saboda ne sharhin al’amuran yau da kullum da Malam Bashir Yahuza Malumfashi yake rubutawa. Sai nake gani ai nima zan iya. Daga bisani kuma har na koma yin rubuce-rubuce a zaurukan sada zumunta, musamman a manhajar fesbuk. Na fi shekara goma sha ina sharhi a jaridu da kafafen watsa labarai, kan al’amuran yau da kullum, musamman abin da ya shafi rayuwar matasa.

Yaushe ka fara tunanin yin rubutun labari na kanka?

Na fara rubutu na kaina tun a shekarar 2024. 

Za ka iya tuna labarin farko da ka rubuta? A kan me labarin yake magana?

Gaskiya na manta da sunan labarin, don a fesbuk na rubuta, amma nasan jigon akan yajin aikin malaman jami’oi ne.

Kana da wasu masu gida ko abokan rubutu da suke taimaka maka da shawarwari yadda za ka gyara rubutunka ko labarin da ka rubuta?

E, tabbas ina da su. Daga ciki akwai wasu ýan jarida guda biyu da nake ji da su sosai, saboda irin gudunmawar da suke ba ni a harkar rubuce-rubuce na, Malam Bashir Yahuza Malumfashi da Malam Abba Abubakar Yakubu, a duniyar rubutu dai ba ni da iyayen gida kamar su. Sai kuma malamata Hadiza D. Ibrahim Auta, da yayata Bilkisu Garba Mai’agogo da ýar’uwata Na’ima Sulaiman Daƙayyawa, da sauran marubuta  dama da nake tura rubutuna su duba min. Alhamdulillah suna bakin ƙoƙarin su.

Wanne irin salon labari ka fi rubutawa, jarumta, almara, soyayya, ko zamantakewa?

Na fi mayar da hankali kan rubutun da ya shafi zamantakewa, don sai wasu muhimman abubuwa sun faru nake rubutu. Wani lokaci kuma ina rubutu akan abin da ya shafi jarumta da soyayya. Akasari dai labaruna sun fi ƙarfi wajen warware matsalolin rayuwa da saƙonni irin na nuni-cikin-nishaɗi.

Yaya alaƙarka da sauran marubuta adabin Hausa?

Alhamdulillah, babu abin da zan ce sai godiya. Ba ni da abin cewa sai yi musu fatan alheri. Ban taɓa faɗa da wani marubuci ba, hasali ma har akwai wasu manyan marubuta da suke girmama ni, saboda kyakkyawar mu’amalar dake tsakanin mu da su.

Ka taɓa wallafa wani daga cikin labaran da ka ke rubutawa zuwa littafi, ko har yanzu a onlayin ka ke fitarwa?

Ban taɓa wallafa labarina zuwa littafi ba, a onlayin nake wallafawa, amma akwai wanda na ke kan rubutawa yanzu, wato Alƙalamina. Labari ne akan wani marubuci da ƙaddara ta faɗa kansa, aka zarge shi da hannu a kisan wani ɗan siyasa, sanadiyar wani littafi da ya rubuta. Binciken ýansanda ya gano cewa salon kisan da aka yi wa mutumin ya yi kama da labarin da marubucin ya wallafa. Don haka sai kotu ta yanke wa marubucin hukuncin ɗaurin rai da rai. In sha Allahu nan da wani lokaci zan kammala rubutawa, kafin a buga.

Kana daga cikin marubuta da ake ganin suna nuna shauƙi kan rubuce-rubuce da son littattafai, me yake ba ka ƙwarin gwiwa cigaba  da nuna soyayyar ka ga littafi?

Bilhaƙƙi, da gaskiya ina ƙaunar littafi. Na yi imanin cewa karatun littafi tamkar makaranta yake, yana koyar da abubuwa da dama waɗanda ɗan’adam yake ƙaruwa da su. Babu shakka, duk mutumin da ya zama mai ilimi sai da ya karanta littafi. Bayan haka, shi littafi wakili ne na marubuci, wanda ko ya mutu za a riƙa amfana da iliminsa, kuma za a riƙa tunawa da shi. 

Ka taɓa samun wata matsala ko saɓani tsakanin ka da wani ko wasu game da harkokin ka na rubutu?

A’a, gaskiya ban taɓa samun wata matsala da kowa ba. Sai dai wasu da ke faɗar maganganu marasa daɗi dake kallon sabgar rubutu a matsayin shirme. Wasu suna ganinka za su fara kiran ka marubuci da zolaya, amma ba na bin ta kansu, don na yi imanin wata rana su da kansu za su tuna abin da suka faɗa, bayan da buri ya cika. In sha Allahu ko a yanzu sai godiya ga Allah, tun da har an kawo lokacin za a gayyace ni gidajen rediyo da jaridu ina bayani akan rubuce-rubuce, ai buri ya cika, tun da duniya ta fara sanin gudunmawar da ka ke bayarwa.

Sakamakon bincike da tattaunawa da ka ke yi da marubuta me ka lura da shi wanda yake ƙarfafa gwiwar marubuta, ko kashe musu gwiwa?

Masu bibiyar labaransu su ne suke ƙarfafa musu gwiwa. Abin ya ke kashe musu gwiwa kuma shi ne rashin tallafi ga masu ƙarfi da mawadata.

Wanne tasiri fasahar AI ta kawo a harkar rubuce-rubuce da ƙirƙirar labari?

Basirar AI ta kawo ci gaba sosai a harkokin rubuce-rubuce. A cikin sauƙi marubuci zai samu bayanai kan yadda zai gina jigon rubutunsa, wanda a baya sai mutum ya wuni yana ta bincike bai gano su ba. Amma a yanzu umarni kawai zai bayar sai ka ga bayanai sun fito. Gaskiya an samu sauƙi sosai. Amma a wata fuskar fasahar AI ta ɓata wasu marubuta, saboda yanzu ba sa iya zama su yi bincike kamar a baya. Sannan dogara da AI ya sa hatta wata Hausar da ake rubutawa za ka ga akwai gwaranci sosai a cikinta.

Ba mu labari ƙungiyar ku ta marubuta maza zalla, me ya sa ku tunanin kafa ƙungiyar, kuma a wanne matakin ƙungiyar take?

Dalilin da ya sa muka kafa ƙungiyar Male Authors Association of Nigeria shi ne haɗa kan marubuta maza waje guda, don a tafi tare da kuma tsira tare. Yanzu haka dai an yi wa ƙungiyar duk wata rijista da ta kamata, kodayake har yanzu ba mu fara gabatar da wasu manyan ayyuka ba, amma muna shirye-shirye in sha Allahu.

Shin kana ganin har yanzu ana samun karsashin son rubutun adabi a wajen maza ko abin ya koma hannun mata?

Akwai karsashin rubutu a wajen maza marubuta, kuma muna nan muna kan cigaba da rubuce-rubucen da muka saba yi bakin rai bakin fama! Abin da ya sa ake ganin mata sun fi maza yawan yin rubutu shi ne su mata suna samun isasshen lokaci a gida, basu cika yawan fita suna gwagwarmayar nema ba, ba kamar yadda mu maza muke yi ba. Don haka suke fin mu samun zarafin yin rubutu.

Akwai da dama marubutan Hausa da yanzu sun koma harkar rubutun fim, sun jingine labarin zube, kana ganin me ya kawo haka?

A wannan tambayar za mu kwana. Da yardar Mai Duka mako mai zuwa za mu fara da amsar tambayar kafin wasu su biyo baya.

By ukarofi

Leave a Reply