Kofin Duniya: Argentina za ta kara da Sifaniya a wasan ƙarshe bayan doke Ingila

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Argentina ta yi nasarar hayewa zuwa zagayen wasan ƙarshe a gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan doke Ingila da ci 2 da 1 a wasan dab da na ƙarshe a ranar Laraba.

Hakan na nufin mai riƙe da kofin za ta kara da ƙasar Sifaniya a wasan ƙarshen a gasar da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka.

Da fari, Ingila ce ta fara zura ƙwallo a wasan a minti na 55 ta hannun ɗan wasa Anthony Gordon, lamarin da ya ba ƙasar damar jan ragamar wasan.

Bayan gurmurzu na tsawon minti 30 ne Argentina ta farke a lokacin da zakaran ɗan ƙwallon duniya Lionel Messi ya ba wa Enzo Fernandez fasin.

Lautaro Martinez ne wanda ya jefa ƙwallo ta biyu a ragar Ingila ta hannun Messi yayin da aka ƙara minti tara bayan kammala mintina 90 ana 1 da 1.

A ranar Talata ne Sifaniya ta doke Faransa da ci 2 da 0 a ɗaya wasan, wanda ya ba ta damar zuwa zagayen ƙarshe tun bayan lashe kofin a shekarar 2010.

By Babaji

Leave a Reply