NAHCON za ta mayar wa alhazan 2026 kuɗaɗen da ba a yi musu hidimarsu ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta tabbatar wa mahajjatan 2026 cewa za ta mayar musu da kuɗaɗensu da suka biya na hidimar da ba a musu ba.

Da yake jawabi a taron ajandar gyara da nazari na masu ruwa da tsaki bayan kammala ayyukan hajjin, Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya ce hukumar ta fara ta fara aiki akan rahotannin kuɗaɗen da aka kashe tare da haɗin-gwiwar hukumomin Saudiyya domin tabbatar da adalci akan aikin hajjin da aka kammala a kwanan nan.

Ya yi gargaɗi ga kamfanonin hidimar hajji na Nijeriya akan cewa lokacin gazawar kammala aikin kwangila ba tare da hukunci ba ya wuce, yana mai cewa wajibi ne a biya kowane mahajjaci da ba a yi masa hidimar da ya biya kuɗi akanta ba.

A cewarsa, an samu nasarori da dama a aikin hajjin 2026 ciki har da tsari mai kyau na jigila, inganta hanyoyin samar da biza ta fagen Nusuk, inganta harkokin lafiya, da kuma haɗin-gwiwa tsakanin NAHCON da hukumomin alhazai na jihohi da kamfanonin jigila.

Haka kuma, ya bayyana cewa, an shirya zaman ne da nufin nazari akan hajjin da aka kammala da kuma samar da hanyoyin inganta hidindimunta.

By Babaji

Leave a Reply