
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta ce har yanzu ba ta soke ko ta haramta sana’ar downloading a faɗin jihar ba.
Hukumar ta bayyana haka ne bayan ta ce ta samu koke-koke daga masu wannan sana’a da shugabanninsu kan rahotannin da ke yawo cewa an hana gudanar da sana’ar downloading a Kano.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce babu wata hukuma da ta tuntube ta ko ta yi shawara da ita kafin a yaɗa irin waɗannan bayanai.
Ta ce masu sana’ar downloading na daga cikin waɗanda take da alhakin sa ido kan ayyukansu bisa dokar da ta kafa ta, tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu ya karya ƙa’idojin gudanar da sana’ar.
Hukumar ta kuma ce ba ta karɓi wani ƙorafi a hukumance ba dangane da lamarin. Sai dai ta ce ta gano wani saƙon murya da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ke zargin wasu masu downloading da yaɗa bidiyoyin tsiraici.
A cewar sanarwar da kakakin hukuma Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya ce binciken matakin farko ya nuna cewa ana zargin muryar da ke cikin saƙon ba daga Jihar Kano take ba, amma hukumar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Hukumar ta ce ta tura jami’anta a ƙananan hukumomi 44 na jihar tare da Babban Kwamitin Sa Ido domin binciken masu yaɗa saƙonni da hotunan da ake zargin sun saɓa wa doka da tarbiyya.
Ta ƙara da cewa har yanzu ba a gano waɗanda ake zargi ba, amma ana ci gaba bincike.
Game da matsayarta kan sana’ar downloading, hukumar ta ce ta yi la’akari da yarjejeniyoyin kasuwanci da wasu masu sana’ar suka ƙulla da masana’antar Kannywood wajen rarrabawa da dillancin fina-finai.
Ta ce, bayan nazari, ta yanke shawarar ci gaba da ba matasa damar gudanar da sana’ar saboda muhimmancinta wajen samar da abin dogaro da kai da bunƙasa tattalin arziki.
Sai dai hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai kan duk wanda aka samu yana amfani da sana’ar wajen yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya ko koyarwar addinin Musulunci.
A ƙarshe, hukumar ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin gwamnati, shugabannin ƙungiyar masu downloading da sauran al’umma domin magance duk wani abu da zai iya bata sunan sana’ar, tare da buɗe ƙofarta ga duk wanda ke da sahihan bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da bin doka da oda.
Hukumar ta bayyana matsayarta ne bayan da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta haramta gudanar da sana’ar ta downloading a Kano.
Mataimakin kwamandan Hisbah na jihar Kano Dr. Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aikawa manema labarai.
Yace sun dauki matakin ne domin kare tarbiyya matasa dake neman lalacewa, sakamakon yadda masu downloading din suke turawa matasa fina-finan batsa.
Sannan ya kuma ce hukuma ba za ta lamunci duk wani abu da zai lalata tarbiyya matasa a jihar Kano ba, ya ce hakan ce ma tasa suka baza jami’ansu a dukkanin kananan hukumomi 44 dake Kano domin Kamo masu kunnen kashi domin gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abun da suka shuka.
