Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗa manyan sakatarori huɗu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya amince da naɗin manyan sakatarori guda huɗu a jihar.

Sun haɗa da Hussaini Hashimu daga ƙaramar hukumar Ɓaure da Abdu Usman daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa.

Sauran sun hada da Dr Sani Suleiman daga ƙaramar hukumar Funtua da Dr Shamsuddeen Yahaya daga ƙaramar hukumar Kankiya.

Sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Falalu Bawale ya ce an naɗa su wannan muƙami bisa imanin cewa za su nuna ƙwarewa, gaskiya da sadaukar da kai da ake buƙata wajen tafiyar da nauyin da aka ɗora masu.

Haka juma gwamna Raɗɗa ya buƙace su da su bada ta su gudunmuwa wajen bunƙasa aikin gwamnatin Jihar.

Dikko Raɗɗa ya yi kira a gare su da nuna ƙwarewa da sadaukar da kai a yayin tafiyar da aikin su.

By ukarofi

Leave a Reply