2027: Jam’iyyu sun shiga tararrabi bayan kotu ta maida wa INEC ikon jaddawalin zaɓe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jam’iyyun siyasa da dama sun shiga cikin yanayin rashin tabbas bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta dawo da jadawalin gudanar da zaɓen 2027 na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), lamarin da ya tilasta wa wasu jam’iyyu sake hanzarta shirye-shiryensu bayan sun sassauta matakai bisa hukuncin da wata kotu ta yanke a baya.

Rahotanni sun nuna cewa Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da ingancin ƙa’idoji da jadawalin da INEC ta tsara domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.

Hukuncin ya mayar da jadawalin ayyukan zaɓe kamar yadda INEC ta tsara tun farko, ciki har da gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu, gabatar da sunayen ’yan takara da sauran matakan da suka shafi shirye-shiryen zaɓe.

Wannan mataki ya sanya wasu jam’iyyun siyasa cikin matsin lamba, musamman waɗanda suka dogara da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a baya, suna zaton sun samu ƙarin lokaci na kammala shirye-shiryensu, sasanta rikice-rikicen cikin gida da tsara dabarun tunkarar zaɓe.

Yanzu da aka dawo da jadawalin INEC, jam’iyyun da suka yi jinkirin shirye-shirye na fuskantar ƙalubalen hanzarta ayyukansu domin kada lokaci ya ƙure musu kafin fara matakan zaɓen.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin hukuncin zai bayyana irin shirin da kowace jam’iyya ta yi, musamman waɗanda har yanzu ba su warware matsalolin shugabanci ko kammala tsarin zaɓen ’yan takararsu ba.

A hukuncin da alƙalan kotun suka cimma baki ɗaya, Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 20 ga Mayu, wanda ya soke wasu sassa na ƙa’idojin zaɓen INEC tare da dakatar da aiwatar da su.

Hukuncin, wanda Mai Shari’a Adebukola Banjoko ta rubuta kuma Mai Shari’a Okon Abang ya karanta, ya bayyana cewa Youth Party (YP) ba ta da hurumin shari’a na ƙalubalantar ƙa’idojin INEC.

Kotun ta ce jam’iyyar ta kasa tabbatar da yadda ƙa’idojin suka shafi mambobinta ko suka hana ta gudanar da zaɓen fidda gwani da gabatar da ’yan takara domin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply