Kaddamar da shirin Gani Ya Kori Ji da aka yi a makon jiya wata muhimmiyar hanya ce ta inganta ɗaya daga cikin raunin da aka daɗe ana gani a tsarin yadda ake gudanar da mulki a Nijeriya—wato sadarwa da jama’a. Ana auna gwamnati ba kawai da yawan ayyukan da ta aiwatar ba, har ma da yadda take iya isar da bayanan waɗannan nasarori ga al’umma. A wannan fanni, shirin da Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Abdulaziz Abdulaziz, ya ƙaddamar ya cancanci yabo.
Manufar shirin na Gani Ya Kori Ji mai sauƙi ce amma mai ƙarfi. Maimakon a buƙaci ‘yan Nijeriya su dogara ga jawabai na siyasa, sanarwar gwamnati ko muhawarar kafafen sada zumunta, shirin yana ɗaukar ‘yan jarida, masu sharhi da sauran masu ruwa da tsaki ya kai su kai-tsaye zuwa wuraren da ake aiwatar da ayyukan gwamnati. Ana ba su damar su duba ayyukan da idanun su, su tantance yadda aka gudanar da su, sannan su ba da rahoto bisa abin da suka gani. Wannan tsarin ya ginu ne kan hujjoji da gaskiya, ba kan farfaganda kaɗai ba.
Ana daɗe ana zargin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa ta yi watsi da Arewacin Nijeriya wajen rabon ayyukan Gwamnatin Tarayya. Ko da kuwa wannan zargin ya samo asali ne daga adawar siyasa ko kuma rashin cikakken bayani, ya samu karɓuwa ne saboda mutane da dama ba su san irin ɗimbin ayyukan more rayuwa da ake aiwatarwa a yankuna ba. Yanzu kuwa rangadin ayyukan ya fara sauya wannan fahimta. Mahalarta shirin Gani Ya Kori Ji sun kai ziyara wuraren ayyuka a jihohin Kano, Kaduna da Katsina, inda suka ga yadda ake zuba jari a hanyoyi, layukan dogo, makamashi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan more rayuwa. Daga cikin manyan ayyukan da suka ja hankali akwai layin dogo na Kano zuwa Maraɗi, da sake gina hanyar Abuja–Kaduna–Kano, da aikin bututun iskar gas na AKK, da hanyar Northern Bypass ta Kano, da hanyar Western Bypass a Kaduna, da layin dogo na Kaduna–Kano, da ayyukan samar da lantarki masu zaman kansu (Independent Power Projects), da manyan ayyukan ban-ruwa da makamashi da na fetur ba.
Ban da Arewacin ƙasar nan kuwa, shirin ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya cewa ana karkata kuɗaɗen da ake samu daga cire tallafin man fetur ne zuwa manyan ayyukan da za su amfani ƙasa na dogon lokaci. Manyan ayyuka kamar Babban Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gina hanyoyi da gadoji cikin Abuja, da gyaran manyan hanyoyi a Arewa-maso-gabas, da sauran ayyukan layin dogo da makamashi, suna nuna cewa gwamnati tana zuba jari sosai a fannin more rayuwa domin bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Haka kuma, ci gaba da aikin sake gina hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kai matakin ƙarshe, ya nuna yadda wasu manyan ayyuka suke samun ƙarancin kulawa daga jama’a fiye da yadda suka dace. Alhali kuwa wannan hanya tana daga cikin mafi muhimmanci a Nijeriya, domin tana haɗa Babban Birnin Tarayya da arewacin ƙasar nan tare da sauƙaƙa zirga-zirgar miliyoyin matafiya, ‘yan kasuwa da harkokin kasuwanci.
Wani darasi da ake iya koya daga shirin Gani Ya Kori Ji ya wuce a nuna ayyukan gwamnati kawai. Ya bayyana giɓin sadarwa da ya zama wajibi gwamnatoci a kowane mataki su magance shi cikin gaggawa. Kyakkyawan mulki ba ya taƙaituwa ga aiwatar da ayyukan kawai; yana kuma buƙatar tabbatar da cewa jama’a sun fahimci yadda ake amfani da kuɗaɗen su. Idan gwamnati ta gaza wajen sadarwa yadda ya kamata, to ji-ta- ji-ta da yarfen siyasa sukan mamaye gurbin gaskiya. Wannan ƙalubale ya fi tsanani a wannan zamani na soshiyal midiya, inda ji-ta- ji-ta take yaɗuwa cikin sauri. Labaran ƙarya suna iya mamaye ainihin nasarorin gwamnati idan ba a samar da isassun bayanai na hukuma ba. Ta hanyar gayyatar masu sa ido masu zaman kan su su ziyarci wuraren ayyukan da idanun su, Gani Ya Kori Ji ya samar da mafita mai amfani. Ganin manyan hanyoyi, layukan dogo, gadoji da cibiyoyin makamashi da ido ya fi ƙarfi a matsayin hujja fiye da muhawarar siyasa marar iyaka.
Shirin ya kuma ƙarfafa dimokiraɗiyya da saka gwamnati ta rungumi ayyukan ta, domin yana ba jama’a damar yin tambayoyi bisa sahihan bayanai game da kuɗin ayyuka, ingancin su, lokacin kammalawa da yadda ake aiwatar da su. Muhawarar jama’a tana zama mai amfani idan ta dogara da hujjoji da za a iya tabbatarwa, maimakon zato ko ra’ayin jam’iyyun siyasa. Masu shirya wannan tsari sun cancanci yabo saboda fara shi da suka yi daga Arewaci, inda kuskuren fahimta game da rabon ayyukan Gwamnatin Tarayya ya fi yawa.
Sai dai bai kamata shirin ya tsaya a nan ba. Ya dace a faɗaɗa shi ya zama wani shirin wayar da kan jama’a na ƙasa baki ɗaya, wanda zai haɗa ‘yan jarida, ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, sarakunan gargajiya, ɗalibai da shugabannin al’umma daga dukkan shiyyoyin siyasar Nijeriya. Duk ‘yan Nijeriya suna da haƙƙin tabbatar da iƙirarin gwamnati da kan su. Duk da haka, rangaɗin ayyuka kaɗai ba zai magance matsalar sadarwar gwamnati gaba ɗaya ba. Dole ne Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su kafa tsayayyen tsarin yaɗa bayanai ga jama’a. Ya kamata ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati su riƙa wallafa rahotannin cigaban ayyuka a kai a kai, tare da hotuna, bayanan kashe kuɗi da lokutan kammalawa. Mulki na zamani yana buƙatar sadarwa mai ɗorewa, ba yaɗa labarai lokaci-lokaci kawai ba.
A ƙarshe, shirin ya sake tabbatar da hikimar karin maganar Hausa da ya samo sunan sa—gani ya kori ji. Ta hanyar maye gurbin maganganun siyasa da hujjojin da za a iya tabbatarwa, shirin ya fara sauya yadda jama’a ke tattaunawa game da shugabanci da bunƙasa ayyukan more rayuwa. Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da wannan shiri tare da faɗaɗa shi, sannan ta ƙara zuba jari wajen wayar da kan jama’a. ‘Yan Nijeriya ba su cancanci hanyoyi, layukan dogo, asibitoci da ayyukan lantarki kawai ba; suna kuma da haƙƙin samun sahihan bayanai cikin lokaci game da yadda ake amfani da dukiyar al’umma. A tsarin dimokiraɗiyya, tsare gaskiya da buɗaɗɗen aiki suna gina amana, amana kuma tana ƙarfafa shugabanci. Haka kuma, al’umma masu cikakken bayani su ne suka fi dacewa su yi hukunci kan gwamnatoci bisa hujjoji, ba bisa ji-ta- ji-ta ba.
