
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Manaja-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Zuba Jari a Man Fetur na Ƙasa (NAPIMS), Alhaji Bala Wunti ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa babu wata hujja a rahoton kuɗi na Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) na 2023 da ke goyon bayan iƙirarin ɓatar Naira tiriliyan 210 daga asusun kamfanin.
Da yake jawabi a gaban kwamitin nazari kan kuɗaɗen NNPCL na majalisar, Bala Wunti ya ce ya bi takardar rahoton kuɗaɗen daki-daki yana nazari a kai bayan kwamitin ya buƙaci hakan, yana mai cewa batun tiriliyan 210 kuskuren bin tsare-tsaren shigarwa ne ba ba wai an samu hujjar ɓatar kuɗaɗen ba ne.
“Na bi wannan takardar shafi bayan shafi. Ba inda aka ambaci tiriliyan N210”, inji Wunti ga sanatoci.
A cewarsa, adadin da ya haifar da tayar da ƙurar ya samu ne bayan haɗe wasu rahotannin kuɗaɗe biyu da da ba a yi haka ba.
Ya bayyana cewa, wani rahoton na kusan tiriliyan N107 ya wakilci wasu ƙananan basusuka da kamfanin yake bi, yayin da tiriliyan N103 ya wakilci kashe-kashen wasu buƙatu daga ɓangaren kamfanin.
Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin majalisar ya gayyaci tsohon shugaban na NAPIMS da ya yi nazari akan rahotannin kuɗaɗen da kuma bayar da ba’asinsa a kai.
