Gwamnatin Kebbi ta yi wa al’ummar garin Gulma ta’aziyya

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta miƙa ta’aziyya ga al’ummar garin Gulma da ke ƙaramar Hukumar Argungu bisa rasuwar mutane takwas da suka rasa rayukansu sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya faru a garin a kwanakin baya.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ne ya isar da saƙon ta’aziyyar a madadin Gwamna Malam Nasir Idris ga iyalan mamatan da ɗaukacin al’ummar ƙasar Gulma.

Sanata Tafida ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da matuƙar baƙin ciki, inda ya buƙaci iyalan waɗanda abin ya shafa da su yi haƙuri tare da karɓar ƙaddarar Allah. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan tare da bai wa iyalansu juriyar jure wannan babban rashi.

Mataimakin gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Gulma cewa gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin farauto duk waɗanda ke da hannu a kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani aikin ta’addanci ko rashin bin doka da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma ba.

Haka kuma, Sanata Tafida ya gargaɗi al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu ko neman ɗaukar fansa, tare da buƙatar duk wanda ke da wani ƙorafi da ya kai shi ga hukumomin da suka dace.

Tun da farko, Shugaban ƙaramar Hukumar Argungu, Honarabul Aliyu Sani Gulma, ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu shanu mallakin wani makiyayi sun shiga gonar Alhaji Aminu Ala tare da lalata amfanin gonarsa.

Ya ce hakan ya haifar da saɓani tsakanin ɓangarorin biyu, inda ake zargin makiyayin ya caka wa manomin wuka a wuya har ya rasu.

A cewarsa, wannan kisan ya fusata wasu mazauna garin Gulma, inda suka taru suka kashe makiyayin tare da ƙona gawarsa. Daga bisani rikicin ya bazu zuwa wasu daga cikin makiyayan da ke yankin.

Ya ƙara da cewa, duk da saurin da jami’an tsaro suka kai wajen shawo kan lamarin, wasu mutum huɗu sun sake rasa rayukansu yayin rikicin. Daga baya kuma an gano gawarwaki biyu a wata gona da ke wajen garin Gulma, lamarin da ya kai jimillar waɗanda suka mutu zuwa takwas, waɗanda suka haɗa da manomi guda da makiyaya bakwai.

Honarabul Aliyu Sani Gulma ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa gaggawar da gwamnatin jihar ta yi wajen ɗaukar mataki da kuma tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Sarkin Kabin Argungu, Mai Martaba Alhaji Samaila Muhammad Mera, wanda Kokanin Kabi, Alhaji Kabiru Abdullahi, ya wakilta, ya bayyana lamarin a matsayin babban abin baƙin ciki a tarihin Masarautar Kabi.

Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan tare da kira ga manoma da makiyaya da su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da juna.

Uban ƙasar Gulma, Alhaji Muhammad Bashar Gulma, ya gode wa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa matakan da suka ɗauka cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da kuma ƙoƙarin da suke ci gaba da yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

A nasa jawabin, wakilin al’ummar Fulani a Gulma, Malam Aliyu Usman, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin, inda ya buƙaci al’umma su karɓi wannan iftila’i a matsayin ƙaddarar Allah, yana mai ambaton ayar Alƙur’ani cewa: “Ba wata rai da za ta mutu sai da izinin Allah.”

Haka kuma, ya yi kira da a rungumi tattaunawa da haƙuri domin kauce wa sake faruwar irin wannan rikici.

By ukarofi

Leave a Reply