Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Zuriyar Ibrahim Ahmadu Mai ƙarfe ta gudanar da taron sada zumunci karo na biyar domin ƙarfafa alaƙar zumunci da kuma tattauna hanyoyin tallafa wa marasa galihu daga cikin zuriyar.
Shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Sadiƙu Sulaiman Yalwa, ya bayyana cewa taron ya zama wata hanya ta haɗa ‘yan uwa da kuma nemo hanyoyin magance matsalolin da suke fuskanta.
Ya ce Ibrahim Mai ƙarfe ya shahara da sana’ar ƙira da ɗinkin kayan sarauta a Kano, kuma zuriyarsa na ci gaba da riƙe kyawawan dabi’unsa na taimakon jama’a da kyautata mu’amala.
Ya ƙara da cewa zuriyar ta bazu a sassa daban-daban na Nijeriya ciki har da Kano da Jihar Yobe.
Alhaji Sadiƙu ya yi kira ga ‘yan uwa su ci gaba da riƙe zumunci tare da gudanar da ayyukan alheri kamar yadda suka gada daga kakanninsu.
