Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jam’iyyun siyasa uku ne har zuwa ƙarshen wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayar ba su kai sunayen ‘yan takararsu na shugaban ƙasa da mataimakansa cikin tsarin lantarkin hukumar ba, gabanin rufe shafin karɓar sunayen da ƙarfe 11:59 na daren ranar Talata.
Wani babban jami’in INEC, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a hukumance, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyun da abin ya shafa sun haɗa da Jam’iyyar APGA, ɓangaren Jam’iyyar PDP da Nyesom Wike ke jagoranta, da kuma ɓangaren Jam’iyyar LP ƙarƙashin jagorancin Nenadi Usman.
Sai dai jami’in ya bayyana cewa kusan dukkan sauran jam’iyyun siyasa masu rajista sun kammala loda sunayen ‘yan takararsu domin babban zaɓen shekarar 2027.
“Ya zuwa yanzu jam’iyyu kusan uku ne kawai ba su loda sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu ba. Su ne APGA, ɓangaren PDP na Wike da kuma ɓangaren LP na Nenadi Usman. Kusan duk sauran jam’iyyu sun kammala gabatar da sunayen ‘yan takararsu,” inji jami’in.
Tun da farko, INEC ta ƙara wa’adin gabatar da sunayen ‘yan takara ne bayan wasu jam’iyyu sun nemi ƙarin lokaci, amma ta jaddada cewa ba za ta sake yin wani ƙarin wa’adi ba.
Ana sa ran bayan rufe shafin karɓar sunayen, hukumar za ta fara tantance bayanan da aka gabatar bisa tanade-tanaden Dokar Zaɓe da ƙa’idojinta.
Bayan ƙarin wa’adin ya ƙare, alamu sun nuna cewa manyan jam’iyyun adawa sun samu damar cika sharuɗɗan gabatar da ‘yan takararsu.
Har zuwa yammacin ranar Talata, babu wata alama da ke nuna cewa an janye sunayen da aka gabatar, yayin da sunayen shugabannin jam’iyyun da INEC ke amincewa da su suka ci gaba da bayyana a shafin hukumar.
A ranar Lahadi ne INEC ta sanar da ƙarin wa’adi zuwa tsakar daren ranar 14 ga Yuli, bayan da ta sauya ranar ƙarshe daga 11 ga Yuli.
Daga cikin jam’iyyun da suka kammala gabatar da sunayen ‘yan takararsu akwai:
Jam’iyyar APC, wadda ta sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima domin neman wa’adi na biyu.
Jam’iyyar ADC, wadda ta gabatar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa.
Jam’iyyar NDC, wadda ta gabatar da Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.
Sai dai majiyoyi daga INEC sun ce akwai wasu jam’iyyu da suka gabatar da sunan ɗan takarar shugaban ƙasa kawai ba tare da na mataimakinsa ba.
Yayin da ake ci gaba da loda sunayen ‘yan takara, har yanzu akwai rashin tabbas kan sunayen ‘yan takarar Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a wasu jihohi kamar Benuwe, Kwara da Nasarawa, inda ake ta cece-kuce kan waɗanda daga ƙarshe suka shiga shafin INEC.
