
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ce kimanin sama da maniyyata aikin hajjin 2026 guda 9,000 ne suka isa birnin Madinah zuwa yanzu.
A cewar bayanai daga jami’an NAHCON a Saudiyya, adadin ya kai haka ne tun daga fara jigilar su a ranar Lahadin da ta gabata.
Hukumomin Saudiyya sun amince da karɓar maniyyata daga Nijeriya guda 50,000 na shekarar 2026.
Waɗancan maniyyata da suka riga suka isa ƙasar, za su yi aƙalla kwana huɗu kafin garzayawa zuwa Makkah domin cigaba da gudanar da ibadar.
Wani bayani da NAHCON ta fitar ya nuna cewa, jirgin farko ya tashi ne a ranar Lahadi, wanda ya yi jigilar maniyyata daga Jihar Kogi su guda 473 zuwa Madinah, waɗanda suka ƙunshi maza 296 da kuma mata 177.
Sai jirgin Flynas da ya ɗimbi guda 418 a Jihar Kebbi da suka haɗa maza 259 da mata 159.
Haka ma MaxAir, wanda ya yi jigilar 560 daga Jihar Nasarawa waɗanda suka haɗa maza guda 381 da mata 179.
A ranar Litinin, wani jirgi a Legas ya yi jigilar maniyyata 315 daga Oyo, inda aka samu maza 155 da mata 160.
