Tinubu ya amince da naɗa Fani Kayode a matsayin jakadan Nijeriya a Afirka ta Kudu

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, a matsayin Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu.

Fani-Kayode ya bayyana cewa an fara nufin tura shi Jamus, amma ya gabatar da bukatar sauya wurin aiki saboda dalilai na kansa, kuma an amince da hakan.

A cewarsa, ya fi son yin aiki a Afirka ta Kudu saboda tana da muhimmanci a nahiyar Afirka, tana da alaƙa da Najeriya, kuma tana dacewa da ra’ayinsa na siyasar Afirka.

Ya kuma bayyana cewa ya yi wannan roƙo ne bayan an sanar da nadinsa na farko, sannan tsohon Ministan Harkokin Waje ya goyi bayan bukatarsa kafin a mika shi ga shugaban ƙasa wanda ya amince.

Fani-Kayode ya gode wa Shugaba Tinubu da tsohon Minista Yusuf Tuggar bisa amincewar da suka yi masa, sannan ya karyata rahotannin da ke cewa Jamus ta ƙi karɓar nadinsa, yana mai cewa labarin ƙarya ne da aka ƙirƙira don bata suna. Ya kuma gode wa Sanata Sam Enang da ya amince da musayar wurin aiki zuwa Jamus.

By Babaji