Mahaifin marigayiya Habila ya nemi Sufeto-Janar ya ba su gawarta don jana’iza

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tanko Habila, wato mahaifin wannan malamar asibitin da ta rasu a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, Mis Mary Habila, ya yi wa Sufeto-Janar na Rundunar ‘Yan sanda ƙorafi, inda ya nemi a ba su gawarta domin yi mata jana’iza.

Habila ya bayyana haka ne ga manema labarai jim-kaɗan bayan miƙa takardar ƙorafin a lokacin da yake tare da matarsa, wasu ‘yan gidansu da lauyoyinsu a ranar Juma’a.

Ya koka akan yadda kusan mako biyu kenan da rasuwar ‘yar tasa, Rundunar ‘yan sanda a Jihar Ebonyi ba su bayar da gawarta a gare su ba domin gudanar da jana’izarta.

A cewarsa, iyalan ba su da niyyar neman a yi bincike akan gawar marigayiyar, yana mai cewa mutuwa na kan kowa kuma a ko’ina mutum zai iya mutuwa.

Wannan yunƙuri na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma suke cece-kuce akan sanin ainihin dalilin da ya sabbaba mutuwar marigayiyar.

Tuni dai hukumomi suka ce ana kan gudanar da bincike akan al’amarin, inda ake sa ran fitar ƙarin bayani a kai da zarar an kammala.

By Babaji

Leave a Reply