
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Kano, ta haramta wa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) aiki a titinan gwamnatocin jihohi, tana mai cewa babu dokar da ta bata ikon aiki a hanyoyin jihohi ko na ƙananan hukumomi.
Kotun ta bayyana wasu harkokin jami’an FRSC a cikin garin Kano a matsayin haramtattu kuma ba bisa doka ba.
Haka kuma, kotun ta ce jami’an hukumar suna tauye ‘yancin masu zirga-zirga da ababen hawa wajen tsayar da su, ƙalubalantarsu da haifar musu da jinkirin zuwa wajen da suka nufa a hanyoyin da suke mallakar birni ne ba tare da amincewar doka ba.
Mai Shari’a M.S. Shuaibu ne ya gabatar da hukuncin a ranar Alhamis a wata ƙara da Lauya Abba Hikima ya shigar akan ayyukan jami’an hukumar tun a watan Yulin 2025.
A yayin hukuncin, alƙalin ya ce hukumar tana aikia wajen wuraren da take da doka ta ba su dama musamman a lokacin da aka ga jami’anta suna tsayuwa a shingen bincike a titinan jiha a Kano suna tsayar da motoci da sunan bincike.
A cewarsa, hakan saɓa wa sashe na 35 da 41 ne na ‘yancin walwala da zirga-zirga na kundin dokar ƙasa ta 1999.
Akan haka ne ya amince wa tabbatar da dukkan buƙatun Abba Hikima ciki har da haramta wa jami’an tsayarwa, cin mutunci ko haddasa jinkiri ga masu ababen hawa a titinan Jihar Kano ba tare da wani izini ba a dokance.
Sannan, alƙalin ya umarci FRSC da ta wallafa saƙon bayar da haƙuri ga wanda ya shigar da ƙarar a wata jaridar ƙasa tare da biyan sa diyyar N800,000.

