Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar sojoji ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su, sun ƙwato dabbobi 56 da aka sace haka kuma sun kama wani da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci a wasu hare-haren da suka gudana a Jihar Katsina.
A cewar rundunar, dakarun sashi na 2 sun ceto mutanen ne yayin wani sintirin yaƙi a ƙaramar hukumar Faskari.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata uku, maza huɗu da yara biyu. Binciken farko ya nuna cewa an yi garkuwa da su ne a kan hanyar Tsafe zuwa Kuchere da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
A cewar daraktan yaɗa labarai na rundunar Lt Colonel Aliyu Danji ya ce waɗanda aka ceto sun shaida wa jami’an tsaro cewa sun tsere daga maɓoyar masu garkuwa da mutanen ne bayan da ‘yan bindigan da ke tsaron su sun yi bacci.
Ya bayyana cewa a halin yanzu mutanen da aka ceto suna hannun jami’an tsaro, kuma ana shirye-shiryen haɗa su da iyalansu bayan duba lafiyar su.
A wani samame na daban da sojojin suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a ƙaramar hukumar Bakori, dakarun sun kai ɗauki bayan samun rahoton wasu masu aikata laifuka na ƙoƙarin sace dabbobi.
Sai dai dakarun sun buɗe wa ‘yan bindigan wuta lamarin da ya tilastawa ‘yan bindiga tserewa cikin daji.
Sojojin sun sami nasarar ƙwato dabbobi 56 da suka haɗa da shanu huɗu da tumaki 52. Ya zuwa yanzu dabbobin na hannun rundunar har zuwa lokacin da za a miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa.
Haka kuma, rundunar ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci a ƙaramar hukumar Danmusa.
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewa, jajircewa da kuma ƙoƙarin da suke yi wajen gudanar da ayyukansu. Ya ce nasarorin sun nuna irin himmar dakarun wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka.
Ya kuma jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da kuma al’umma masu bin doka.
Ya ce manufar rundunar ita ce ci gaba da yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane, satar dabbobi da sauran laifukan tsaro har sai an samu zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Yammacin Najeriya.
