Ta yi rashin lafiya gabanin rasuwarta, ku tambayi saurayinta – Ministan Ayyuka kan mutuwar ma’aikaciya Habila a gidansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya magantu game da mutuwar malamar asibiti, Mary Habila, inda ya ce ta yi fama da wani rashin lafiya gabanin rasuwarta, lamarin da ya tayar da sabon batu akan abin da ya sababba mutuwarta.

Umahi ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Alhamis, inda ya ce marigayiyar ta yi aiki da shi na tsawon kusan shekaru uku kuma kamar ‘ya take a wajensa da iyalansa.

Ya ce, duk wanda yake son ƙarin bayani akan mutuwarta zai iya tuntuɓar saurayinta, wanda ta yi waya da shi gabanin ta rasu.

Kalaman ministan na zuwa ne a daidai lokacin al’umma suka riƙa cece-kuce akan al’amarin da kiraye-kirayen lallai a gudanar da bincike akan rasuwar Habilar, wadda aka samu ta rasu a gidan ministan da ke garin Uburu na Ƙaramar Hukumar Ohaozara da ke Jihar Ebonyi a ranar 27 ga Yuni.

Habila, wadda ma’aikaciya ce a Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya ta David Umahi da ke Ebonyi, tana ɗaya daga cikin tawagar lafiya da aka naɗa domin su kula da lafiyar ministan, kuma tana cikin waɗanda suka yi masa rakiya zuwa mahaifarsa a lokacin da al’amarin ya faru.

A cewarsa, marigayiyar ta yi fama da wani rashin lafiya da shi ya ɗauki nauyin jinyarta a Turkiyya, inda ya ƙara da cewa ta yi magana da saurayinta ta waya gabanin rasuwarta har take faɗa masa cewa tana fama haɓo.

By Babaji

Leave a Reply