
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da wasu mutane uku bisa zargin su da hannu a garkuwa da ɗalibai da malaman makarantar Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo da aka ceto a kwanan nan.
Mutanen sune Abdulrazak Umar da aka sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa da aka sani da Yunusa bin Musa, da kuma Shamsu Adamu Sani da ya shahara da Abu Itisar.
A ranar 15 ga watan Mayu ne wasu dandazon ‘yan bindiga suka kai hari a makarantu guda uku, inda suka yi awon-gaba da ɗalibai da dama da malamai. Ɗaya daga cikin malaman mai suna Michael Oyedokun ya rasu a hannun ‘yan ta’addar bayan datse kansa da aka yi.
Mutanen sun shaƙi iskar ‘yanci ne bayan shafe kwanaki 56 a daji. An sako su ne bayan wani atisayen haɗakar hukumomin tsaro, inda a yayin haka ne wasu jami’ai suka rasa rayukansu.
A ranar Juma’a, Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙarar tuhume-tuhume guda goma akan waɗanda ake zargin a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Mutane ukun, waɗanda dukkansu ‘yan Ƙaramar Hukumar Sulejan Jihar Neja ne, ana zargin su da kitsa makirci da wani Muhammad Sani, Jibril Mohammed da Ibrahim Khabab a tsakanin Junairu da Mayu 2026 domin su yi garkuwa da ɗalibai da malamai a Jihar Oyo, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 26 na dokokin haramcin ta’addanci a ƙarƙashin kundin dokar ƙasa.
Haka kuma, ana zargin su da taimaka wa aikin garkuwar da kuma ɓoye bayanansu da ayyukan kitsa makircin duk da cewa suna sane da shirin da wasu laifuka da suka ci karo da dokokin haramta ayyukan ta’addanci da taimaka wa masu aikatawa.
