Hare-haren Baƙin Haure: Oshiomhole ya nemi Nijeriya ta kori MTN da DSTv

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sanatan mai wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Adams Oshiomhole, ya yi kira ga gwamnati da ta soke lasisin kamfanonin Afirka ta Kudu da ke aiki a Nijeriya, ciki har da MTN da MultiChoice, sakamakon sabbin hare-haren ƙiyayyar baƙi da ake kai wa ‘yan Nijeriya a ƙasar Afirka ta Kudu.

Kiran nasa ya zo ne yayin da Majalisar Wakilai ta ƙasa ta yi Allah-wadai da sabon tashin hankali, tare da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan gaggawa na diflomasiyya da kariya domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya a ƙasashen waje.

Yayin da yake jawabi a zauren majalisa, Oshiomhole ya jaddada cewa ya kamata Nijeriya ta mayar da martani mai ƙarfi, yana mai nuni da muhimmancin amfani da ƙa’idar “ramawa daidai” a harkokin hulɗar ƙasashen duniya.

Ya ce, lokaci ya yi da ‘yan majalisa za su wuce nuna alhini kawai, su ɗauki matakai masu tsauri domin kare martaba da rayuwar ‘yan ƙasa.

Tsohon gwamnan Jihar Edo ya kuma ba da shawarar cewa Nijeriya ta ƙwace ikon kamfanin MTN tare da soke lasisinsa, yana mai zargin cewa kamfanin na mayar da ɗimbin riba zuwa ƙasarsa ta asali.

Bayan haka, ya buƙaci a sake nazari kan ayyukan kamfanonin Afirka ta Kudu da ke cin gajiyar kasuwar Nijeriya, yayin da ake zargin ‘yan Nijeriya na fuskantar tsangwama a ƙasar su.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun damuwa kan tsaron ‘yan Nijeriya a ƙasashen waje, musamman a Afirka ta Kudu, inda hare-haren wariyar ƙabila ke ci gaba da tayar da hankali.

By ukarofi