Ra’ayin Manhaja

Sababbin hafsoshin Buhari

An daɗe ana kira da roƙo ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauya manyan hafsoshin sojan ƙasar nan masu jagorancin rundunonin tsaro, amma ya na ƙi. Sai da ta kai Majalisar Tarayya ta zartar da ƙudirori a kan lallai ne Shugaban ya kori hafsoshin, amma dai maganar ta wuce ta bayan kunnen sa. Dalilai biyu su ka sanya aka riƙa yi masa wannan kiran. Na farko shi ne, wa’adin hafsoshin ya wuce, har ma ana ganin sun fara cin wa’adin wasu hafsoshin domin tun a cikin 2015 aka naɗa su. Dalili na biyu kuma shi ne gazawar da ake ganin…
Read More