A da can, ana kallon A-Kurkura a matsayin wani maganin gargajiya da ake amfani da shi wajen rage ciwon haƙori, mura, gajiya da wasu ƙananan cututtuka. Amma a yau, abin da aka fara da sunan magani ya fara rikiɗewa zuwa wata babbar matsalar zamantakewa da lafiyar jama’a, musamman a Arewacin Nijeriya.
Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda matasa, mata, dattawa har ma da masu sana’o’i suka rungumi amfani da A-Kurkura ba wai don magani kawai ba, har ma domin samun kuzari, nishaɗi ko kuma ƙara ƙarfin jiki. Wasu sun kai matsayin da ba za su iya gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba sai sun yi amfani da shi. Wannan shi ne matakin da masana kiwon lafiya ke kira ‘dogaro da sinadari’, wato addiction.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda masana lafiya da jami’an hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ke ci gaba da bayyana cewa wasu nau’ikan A-Kurkura na ɗauke da sinadarai masu haddasa maye da lalata kwakwalwa. Binciken ɗakunan gwaje-gwaje ya nuna cewa a wasu lokuta ana cakuɗa tabar wiwi, opium da sauran sinadarai masu haɗari a cikin wannan ruwa da ake tallatawa a matsayin magani.
Idan har bayan kurkurawa mutum kan shiga amai, jiri, gudawa, rasa nutsuwa ko ma faɗuwa sumamme, to wajibi ne al’umma ta tambayi kanta ko wannan magani ne ko kuma wata hanya ce ta daban ta shigar da miyagun ƙwayoyi cikin jiki.
Babbar matsalar ita ce yadda ake sayar da A-Kurkura cikin sauƙi a kasuwanni, tashoshin mota da ƙananan shaguna ba tare da wata cikakkiyar kulawa ba. Yayin da hukumomi ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da tabar wiwi, tramadol da sauran miyagun ƙwayoyi, A-Kurkura na ci gaba da samun karɓuwa a tsakanin jama’a cikin sigar da mutane da dama ba sa ɗaukarsa a matsayin barazana.
Abin takaici ne yadda wasu matasa ke amfani da shi domin samun kuzarin zuwa tarukan siyasa ko gudanar da ayyuka na tsawon lokaci. Haka kuma yadda wasu mata da dattawa suka fara dogaro da shi domin rage gajiya ya nuna cewa matsalar ta wuce iyakar wani rukuni na jama’a.
Haƙiƙa, ba za a yi watsi da yiwuwar akwai wasu nau’ikan magungunan gargajiya masu amfani ba. Amma duk wani sinadari da ba a tantance shi ba, wanda kuma ke haddasa sauye-sauye ga tunani da halayyar mutum, ya kamata ya zama abin dubawa ga hukumomin lafiya da tsaro.
Lokaci ya yi da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA), Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), ma’aikatun lafiya da shugabannin al’umma za su haɗa hannu wajen gudanar da bincike mai zurfi kan A-Kurkura. Haka kuma ya zama wajibi a wayar da kan jama’a game da haɗarin amfani da duk wani magani da ba a tabbatar da ingancinsa ba.
Makomar matasa ita ce makomar ƙasa. Idan aka bari wata sabuwar hanyar shaye-shaye ta samu gindin zama cikin al’umma saboda sakaci ko jahilci, to nan gaba za a iya fuskantar matsalar da za ta fi ƙarfin gyara.
A-Kurkura na iya zama magani ga wasu, amma idan aka yi la’akari da gargaɗin masana da hukumomi, akwai alamun cewa yana ƙara zama wata sabuwar annoba da ke barazana ga lafiyar al’umma. Don haka, ya dace gwamnati, iyaye, malamai da shugabannin addini su ɗauki matakin gaggawa kafin lamarin ya fi ƙarfin magani.
