Daga AISHA ASAS
Waƙar ‘Dai Dai’ ta mawaƙin Najeriya Burna Boy da fitacciyar mawaƙiya ‘yar Colombia Shakira ta ci gaba da riƙe matsayi na ɗaya a jadawalin Billboard Global 200, inda ta shafe mako na biyar a jere tana kan gaba.
Billboard ta bayyana cewa waƙar, wadda ta kasance waƙar gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, ta ci gaba da samun gagarumar karɓuwa duk da cewa an kammala gasar tun kusan wata ɗaya da ya wuce.
A jadawalin da aka sabunta a ranar 18 ga Agusta, Dai Dai ta ci gaba da kasancewa a matsayi na ɗaya.
Bayanan Luminate da Billboard suka yi amfani da su sun nuna cewa waƙar ta samu kusan rafukan sauraro miliyan 44.1 da kuma sayar da kwafi 6,000 a duniya a cikin makon da ya ƙare ranar 13 ga Agusta. A jadawalin Billboard Global Eɗcl. U.S., waƙar ta kuma shafe mako na takwas a matsayin ta ɗaya.
A yayin gasar cin kofin duniya, Burna Boy da Shakira sun yi waƙar a wajen babban taron ƙarshe na gasar, lamarin da ya ƙara ba waƙar damar samun ɗimbin masu sauraro a duniya. Duk da kammala gasar, waƙar ta ci gaba da samun karɓuwa a kafafen sauraron waƙa da rediyo.
Wannan nasarar ta ƙara tabbatar da yadda haɗin gwiwar mawaƙan Afirka da fitattun mawaƙa daga wasu sassan duniya ke samun karɓuwa a kasuwannin waƙa na duniya, yayin da Burna Boy ke ci gaba da wakiltar Afrobeats a manyan dandamalin waƙoƙi na ƙasa da ƙasa.
