Daga AISHA ASAS
Fitacciyar jarumar Nollywood kuma mai shirya fina-finai, Funke Akindele, ta bayyana jerin fitattun jaruman da za su fito a sabon fim ɗinta mai suna ‘The Four: No One Fights Alone’.
Fim ɗin, wanda za a fara nuna shi a gidajen sinima a faɗin duniya ranar 11 ga Disamba 2026, ya haɗa manyan sunaye daga Nollywood, ciki har da Funke Akindele, Bisola Aiyeola, Chioma Akpotha, Waje, Richard Mofe-Damijo, Timini Egbuson, Lateef Adedimeji, Ali Nuhu, Uzor Arukwe, Ronke Oshodi-Oke da Wunmi Toriola.
Haka kuma fim ɗin zai kunshi fitattun mawaƙa da masu nishaɗi, ciki har da Waje da Shoday, yayin da wasu daga cikin jaruman za su taka rawar mata huɗu da labarin fim ɗin ya fi karkata a kansu.
A cewar bayanan da aka fitar, The Four labari ne da ya shafi abota, uwa da ‘ya, juriya da kuma irin ƙarfin da mata ke samu wajen fuskantar ƙalubale. Labarin fim ɗin ya shafi Esosa da wasu mata uku da suka haɗa kai domin yaƙar wani babban ƙalubale da ya shafi makomar wani matashi da suke ƙauna.
Fim ɗin zai kasance ɗaya daga cikin manyan ayyukan Funke Akindele da ake sa ran za su shiga gidajen sinima a lokacin hutun ƙarshen shekara, lokacin da fina-finan Nollywood ke yawan samun ɗimbin masu kallo. An riga an sanar da cewa FilmOne Entertainment ne zai rarraba fim ɗin a gidajen sinima.
