Tirka-tirkar canjin mataimakin gwamnan Jihar Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Tun bayan shari’ar da ta biyo bayan zargin takardun shaidar kammala karatun sakandare na Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Argungu, Tafidan Kabi, bayan babban zaɓen shekarar 2023, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da ke adawa da shi suka yi ta ƙoƙarin ganin an sauya shi daga mukaminsa.

Shari’ar ta haifar da zazzafar taƙaddama, inda ’yan jam’iyyar PDP suka kalubalanci nasarar Gwamna Malam Nasir Idris da mataimakinsa Sanata Umar Abubakar Argungu.

Yanzu dai rahotanni sun tabbatar da cewa an sauya Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Argungu, inda aka maye gurbinsa da Ibrahim Augie.

Sai dai wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, musamman saboda wasu na ganin cewa sauya Sanata Umar Abubakar na iya yin tasiri a babban zaɓen shekarar 2027 da ke gabatowa.

Wasu daga cikin masu adawa da sauyin na ganin cewa Sanata Umar Abubakar yana da karɓuwa sosai a yankin Argungu, yayin da sabon wanda aka maye gurbinsa da shi, Ibrahim Augie, bai kai shi gogewa da karɓuwa a fagen siyasa ba.

Wasu majiyoyi na kusa da Sanata Yahaya Abdullahi, mai wakiltar Kebbi ta Arewa a Majalisar Dattawa, da kuma ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kebbi mai wakiltar ƙaramar hukumar Argungu, Honarabul Umar Na-Amore, sun nuna rashin amincewarsu da sauyin, bisa fargabar illar da hakan ka iya haifarwa a zaɓen da ke tafe.

Wani daga cikin ’yan siyasar da ke goyon bayan Sanata Umar Abubakar Argungu ya bayyana rashin jin daɗinsa, inda ya ce idan har aka tabbatar da sauyin, wasu daga cikin magoya bayan Sanatan ba za su sake zaɓar APC ba.

Ya ce ko da kuwa suna cikin jam’iyyar, kuma shugaban siyasarsu ya nemi su yi haƙuri, za su iya bijire masa.

Haka kuma, wasu daga cikin waɗanda ke neman kujerar sun bayyana cewa idan Ibrahim Augie ne za a bai wa mukamin, sun gwammace a bar Sanata Umar Abubakar Argungu ya ci gaba da kasancewa mataimakin gwamna, musamman saboda rashin isasshiyar gogewar Ibrahim Augie a fagen siyasa.

Sai dai wani jigo a siyasar yankin, Malam Nasir Ahmed, ya ce sauyin ba yana nufin cin zarafin Sanata Umar Abubakar Argungu ba ne, domin kowa ya san irin karɓuwar da yake da ita da kuma gudunmawar da yake bayarwa.

A cewarsa, an ɗauki matakin ne domin kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da matsala bayan kammala zaɓen.

Daga cikin waɗanda aka ce sun nemi mukamin akwai Muhammed Bello Dantani, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi a lokacin mulkin Sanata Adamu Aliero; Honarabul Sama’ila Bui, tsohon Kwamishinan Kuɗi; Honarabul Sama’ila Abdulmumini Kamba (Ganda), tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi; Ibrahim Augie, tsohon Kwamishinan Kuɗi a lokacin mulkin Sanata Atiku Bagudu; da Nura Usman Kangiwa, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kebbi mai wakiltar wata ƙaramar hukuma a yankin Arewa, da sauran masu neman kujerar.

A baya-bayan nan ne kuma aka gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, inda Alhaji Kabiru Sani Giant, mai bai wa Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin siyasa, ya ce an shirya taron ne domin dinke duk wata baraka da ke cikin jam’iyyar tare da bai wa waɗanda ke ganin ba a yi musu adalci ba damar bayyana matsalolinsu.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC a shirye take ta rungumi kowa domin tafiya tare.

By ukarofi