Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sa’o’i kaɗan bayan tabbatar da nasarar samun wa’adin mulki na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Adeleke, wanda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, a zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Yayin da yake gode wa Shugaba Tinubu bisa kiran waya da ya yi masa domin taya shi murna, Adeleke ya bayyana shugaban ƙasar a matsayin “ɗan Osun”, tare da yaba masa kan rawar da ya taka wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci.
Adeleke ya ce: “A wannan lokaci, ina matuƙar godiya ga Mai Girma Shugaban ƙasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu, bisa irin goyon bayan da ya bayar wajen tabbatar da gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci. Shugaban ƙasa ɗan Osun ne, kuma ina sake tabbatar da goyon bayana gare shi domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.”
Sai dai wannan matsaya tasa ta jawo martani iri-iri, musamman daga wasu magoya bayansa da ’yan adawa, waɗanda suka ɗauki zaɓen Osun a matsayin fafatawa tsakanin Adeleke da ƙungiyarsa ta siyasa da kuma tsarin mulkin APC.
Daga baya Adeleke ya bayyana cewa goyon bayansa ga Tinubu bai samo asali daga wata yarjejeniya ta siyasa da aka cimma tsakaninsu dangane da zaɓen Osun ba.
Da aka tambaye shi ko ya cimma wata yarjejeniya da Shugaban ƙasa, Adeleke ya ce: “A’a, ban taɓa cimma wata yarjejeniya da Shugaban ƙasa ba.”
Ya ce goyon bayansa ya samo asali ne daga kasancewar Tinubu ɗan Yarbawa ne daga yankin Kudu maso Yamma, da kuma burinsa na ganin an ci gaba da ayyukan gwamnatin tarayya da aka fara a yankin.
A cewarsa, “Goyon bayana ya samo asali ne daga kasancewarsa ɗan Yarbawa kuma daga Kudu maso Yamma. Ina ganin dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya da ya fara ginawa, ina son in ƙarfafa shi kada ya manta da Kudu maso Yamma.”
Ya ƙara da cewa tun da ɗan Yarbawa ne ya samu wa’adin mulki na farko, kamata ya yi a sake ba shi dama domin ya ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ya fara.
Da aka tambaye shi ko zai yi wa Tinubu kamfen a 2027, Adeleke ya amsa da cewa: “Big time, I will”, ma’ana zai yi hakan sosai.
Wannan matsaya ta Adeleke ta jefa shi cikin wani yanayi na siyasa mai ban mamaki, domin kuwa ya kayar da jam’iyyar Tinubu a Osun, amma a matakin tarayya yana nuna cikakken goyon bayansa ga Shugaban ƙasa.
Wasu daga cikin masu sukar Adeleke sun bayyana rashin jin daɗinsu kan goyon bayan da ya nuna wa Tinubu, inda suka ce hakan na iya nuna cewa ya sauya dabarar siyasarsa nan take bayan kammala zaɓen.
Wani mai amfani da kafar ɗ mai suna @Maiksmoney ya zargi gwamnan da fifita ƙabilanci kan cancanta.
Shi ma Abiola Oshodi ya soki Adeleke bisa goyon bayan Tinubu bayan da magoya bayansa suka yi fafutuka domin kayar da APC a zaɓen.
Wani mai amfani da ɗ mai suna @oteessolutions1 kuwa ya tambayi dalilin da ya sa Adeleke ya gode wa Shugaban ƙasa kan gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci, yana mai cewa INEC ce ke da alhakin gudanar da zaɓe.
Sai dai wasu sun yi kira ga jama’a da kada su ɗauka cewa goyon bayan Adeleke kai tsaye yana nufin mutanen Osun za su zaɓi Tinubu a 2027.
Ba dukkan martanin da aka samu ba ne suka mayar da hankali kan batun ƙabila ko akida. Wasu masu sharhi sun fassara matakin Adeleke a matsayin wata dabara ta siyasa domin ci gaba da kyakkyawar alaƙa da gwamnatin tarayya.
Olusegun Adepoju ya ce Adeleke na taka-tsantsan ne, musamman ganin yiwuwar APC ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu.
A cewarsa, kyakkyawar alaƙar Adeleke da Tinubu na iya zama mai muhimmanci idan har aka samu shigar da ƙarar zaɓen gaban kotu.
Sai dai wasu kuma sun ce goyon bayan Adeleke bai kamata ya zama dalilin da zai kayyade yadda ’yan Nijeriya za su kaɗa ƙuri’arsu a 2027 ba, domin a ƙarshe ikon zaɓe yana hannun masu katin zaɓe.
Adeleke ya lashe wa’adin mulkinsa na farko a shekarar 2022 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ya kayar da tsohon Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola na APC.
Sai dai bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP, Adeleke ya fice daga jam’iyyar ya koma Accord Party gabanin zaɓen gwamnan Osun na 2026.
A zaɓen da aka gudanar, Adeleke ya samu ƙuri’a 511,067, yayin da ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu 444,815. ɗan takarar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’a 17,180.
Adeleke ya lashe ƙananan Hukumomi 19 daga cikin 30 na Jihar Osun, yayin da Oyebamiji ya samu nasara a ƙananan Hukumomi 11.
