Amurka da Koriya ta Kudu sun rage tsawon babban atisayen sojinsu na shekara-shekara, bayan umarnin Shugaban Amurka Donald Trump na a rage yawan atisayen.
Atisayen Ulchi Freedom Shield, wanda aka fara a wannan makon, yanzu za a kammala shi bayan kwanaki biyar maimakon kwanaki 11 da aka tsara a baya. Haka kuma an rage wasu daga cikin atisayen sojin kasa.
Matakin ya zo ne bayan Trump ya nuna cewa ba ya son yawan atisayen soji da Koriya ta Kudu, yana mai cewa yana son sake buɗe ƙofar tattaunawa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.
Sai dai wasu masana tsaro sun yi gargaɗin cewa rage irin waɗannan atisaye na iya shafar shirye-shiryen sojin ƙasashen biyu da kuma karfin kawancen da ke tsakaninsu. Koriya ta Arewa kuwa ta daɗe tana kallon atisayen Amurka da Koriya ta Kudu a matsayin barazana ga tsaronta.
