Turkiyya ta yi kakkausar suka ga hare-haren sama da Isra’ila ta kai wani sansanin soji a Syria, tana mai cewa bayanan da Isra’ila ta bayar wajen kare matakin nata ba su da tushe.
Isra’ila ta kai hare-hare takwas kan sansanin Abu al-Duhur da ke kusa da Aleppo a ranar Talata, a cewar kafafen yaɗa labaran Syria. An ce hare-haren sun shafi titin saukar jiragen sama da wasu wuraren ajiye kayan aiki, amma ba a samu rahoton mutuwar mutane ba.
Isra’ila ta ce matakin nata ya kasance ne saboda damuwar cewa Syria na shirin barin sojojin Turkiyya su yi amfani da sansanin, abin da ta ce zai iya zama barazana ga tsaron Isra’ila.
Turkiyya ta yi watsi da wannan bayani, tana mai zargin Isra’ila da amfani da hujjojin da ba su da tushe wajen kare abin da Ankara ta kira matakin da ba ya taimakawa wajen samun zaman lafiya a yankin.
Amurka ma ta bayyana harin a matsayin karin tashin hankali da ba dole ba, yayin da Washington ke ƙoƙarin samar da wata hanyar rage yiwuwar arangama tsakanin Isra’ila, Syria da Turkiyya.
