Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar siyasa ta Matawalle, mai take Matawalle Political Movement MPM a Zamfara ta taya fitattun ‘ya’yan jihar Zamfara guda biyar murna kan shigar da su cikin Majalisar kamfen ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙungiya, Yusuf Idris Gusau, ya sanya wa hannu a yau Asabar a Gusau, ƙungiya ta ce naɗin ya ƙara sanya Zamfara a kan matsayi mai kyau a siyasar ƙasa.
Kungiyar ta bayyana naɗin a matsayin wani muhimmin abin girmamawa ga gudummawar da jihar ta bayar ga APC.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya naɗa Sanata Abdulaziz Yari Abubakar a matsayin darakta janar, Hon. Ministan Tsaro, Dr. Bello Mohammed Matawalle a matsayin mataimakin darakta, a kan harkar tsaro da leƙen asiri, yayin da Gwamna Dauda Lawal zai yi aiki a matsayin memba na kwamitin masu ruwa da tsaki.
“Muna kuma godiya da yadda tsohon gwamna Ahmad Sani Yerima da tsohon gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi suka samu shiga cikin majalisar gangamin yaƙin neman zaɓen” .
Ƙungiyar MPM ta nuna matuƙar godiya ga Allah da ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zurfin tunani wajen naɗin fitattun jigon siyasa a Jihar ta Zamfara.
Ƙungiyar ta ce tunda Zamfara ta samu DG, Mataimakin Darakta na Tsaro, da sauran manyan mambobi, Shugaba Tinubu tabbas yana kan hanyarsa ta zuwa wa’adi na biyu.
Kungiyar ta tabbatar wa Shugaban ƙasa cewa sabbin ‘Yan Zamfara da aka naɗa, za suyi iya ƙoƙarin su wajen gani shugaban ƙasa da kuma APC a babban zaɓe mai zuwa sun samu nasarar da ake buƙata.
