Ilimi ba ya cika sai da tarbiyya — Shugaban Makarantar Guidway

Spread the love

Daga WAKILINMU

Shugaban Matarantar Guidway Islamic Science Academy, da ke Layin Awe Road, Kinkinau a Jihar Kaduna, Malam Muhammad Surajo Inace, ya yi kira ga iyaye da su ƙara mayar da hankali kan tarbiyya da karatun ’ya’yansu.

Malam Surajo ya ce, duk wanda Allah Ya azurta shi da ’ya’ya, ya samu babbar ni’ima da alheri, don haka ya kamata iyaye su kasance masu kulawa da tarbiyya da kuma ilimin ’ya’yansu.

Ya ja hankalin iyaye da kada su ɗora wa malamai alhakin tarbiyyar ’ya’yansu su kaɗai, domin iyaye ma suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗa ya tashi cikin tarbiyya nagari.

Ya ce, “Ba za a ce malamai su kaɗai ne za su ɗauki nauyin tarbiyyar yara ba. Iyaye suna da babban tasiri wajen gina halayen ’ya’yansu.”

Shugaban makarantar ya kuma yi kira ga ɗalibai da su kasance masu tawali’u, girmama iyayensu da yi musu biyayya.

Ya ce idan ɗalibai suka rungumi waɗannan halaye, za su samu damar zama ’ya’ya nagari kuma su samu nasara a duniya da lahira.

Tun da farko, an gabatar da bikin saukar Alƙur’ani Mai Girma, inda aka karrama ɗalibai 10 da suka kammala haddar Alƙur’ani a makarantar.

Mutane da dama da suka halarci taron sun yaba da irin ƙoƙarin da ɗaliban makarantar suka nuna, musamman wajen karatun Alƙur’ani da sauran harkokin ilimi.

A ƙarshe, Shugaban Makarantar, Malam Muhammad Surajo Inace, ya yi fatan alheri ga dukkan mahalarta taron, tare da addu’ar Allah Ya sanya abin da aka gudanar ya zama sanadin ƙarin ilimi, tarbiyya da ci gaba ga ɗalibai da al’umma baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply