Trump ya musanta tattaunawa da Iran, yayin da rikicin Hormuz ke ƙara tsananta

Spread the love

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Amurka da Iran, yayin da Tehran ta ce har yanzu mashigar ruwan Hormuz a rufe take, lamarin da ya sake jefa shirin kawo ƙarshen rikicin ƙasashen biyu cikin rashin tabbas.

Trump ya bayyana hakan ne ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, inda ya ce babu wata tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Washington da Tehran. Ya kuma dage cewa mashigar Hormuz a buɗe take, kuma ana iya zirga-zirgar jiragen ruwa a cikinta.

Sai dai Iran ta musanta hakan, inda ta ce ba za ta buɗe mashigar ba har sai Amurka ta cika wasu sharuɗɗan da suka haɗa da kawo ƙarshen katangar da ta kafa wa tashoshin jiragen ruwan Iran, ɗage takunkuman man fetur, sakin ƙadarorin Iran da aka daskarar da kuma dakatar da barazanar kai hare-haren soji.

Sabani kan makomar Hormuz ya ƙara bayyana ne bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wutar da ƙasashen biyu suka cimma. A ranar Litinin ne wa’adin kwanaki 60 da aka ware domin cimma wata yarjejeniya mai fadi kan shirin nukiliyar Iran da takunkuman Amurka ta ƙare, ba tare da an cimma matsaya ba.

A halin da ake ciki, zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ta ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas. Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta Birtaniya ta ce wani jirgi ya gamu da wani makami da ba a tantance ba yayin da yake fita daga Hormuz, lamarin da ya lalata dakin injinsa tare da jikkata wani daga cikin ma’aikatansa har ya rasa ransa.

Haka kuma, Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta gano makamai masu linzami guda biyu da aka harba daga Iran, waɗanda ta ce suna iya yin barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa, duk da cewa  Iran ta yi watsi da zargin, tana mai cewa babu gaskiya a cikinsa.

Duk da tsauraran kalaman da ke fitowa daga ɓangarorin biyu, Iran ta ce har yanzu ƙofar tattaunawa da ita a buɗe take. Mohammad Mokhber, mai ba da shawara ga Jagoran Iran, ya ce tattaunawa da Amurka ba ta nufin mika wuya, yana mai cewa Tehran za ta ci gaba da kare tsaronta da muradunta.

Rikicin ya kuma ci gaba da yin tasiri a kasuwannin duniya, musamman kasuwar mai. Farashin danyen mai na Brent ya taba kaiwa dala 126 kan ganga tun bayan fara yakin, yayin da ya rufe kasuwar Talata a sama da dala 91.

Mashigar Hormuz na da muhimmiyar rawa ga kasuwancin makamashi na duniya, domin kafin rikicin, kusan kashi ɗaya cikin biyar na danyen mai da iskar gas mai narkewa da ake safarawa a duniya na ratsa ta cikinta.

By ukarofi

Leave a Reply