An kama wata sabuwar amarya mai shekaru 19, Aisha Musa, bisa zargin sanya wa mijinta guba a cikin abincinsa a ƙauyen Gwamna, ƙaramar Hukumar Bauchi ta Jihar Bauchi.
An ce lamarin ya faru ne kwanaki 40 kacal da auren ma’auratan.
Rahotanni sun ce bayan mijin ya ci abincin ya fara fama da rashin lafiya.
An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, inda yake karɓar magani.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da kama matar da ake zargi da hannu a lamarin.
Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 12 ga Agusta, 2026, da misalin ƙarfe 3:15 na rana, bayan rundunar ta samu kiran neman agaji daga wata mata da ba ta bayyana sunanta ba da ke zaune a yankin Wunti Dada na Bauchi.
A cewarsa, jami’an ’yan sanda na Sashen ‘C’ da ke Tafawa Balewa Estate sun gaggauta zuwa wurin, inda suka ɗauki wanda abin ya shafa zuwa asibitin koyarwa domin samun kulawa.
Ya ce, likitan da ke kula da shi ya bayyana cewa halin lafiyar mutumin ya daidaita.
Habib ya ƙara da cewa jami’an sun kama wadda ake zargin, inda a lokacin da ake yi mata tambayoyi ta yi wani bayani da ke alaƙanta ta da zargin.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun kuma ƙwato wata kwalbar da babu komai a cikinta da ake zargin an ajiye guba a ciki, da kuma ragowar abincin da mutumin ya ci, domin amfani da su a matsayin hujjojin bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin tura shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin gudanar da cikakken bincike a ɓoye.
Kakakin rundunar ya ce za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
