Gajerun wasannin kwaikwayo sun fara jan hankalin Hollywood

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Masana’antar fina-finan Hollywood na fara ƙara karkata zuwa wani sabon salo na shirye-shiryen bidiyo gajeru da ake kallo kai tsaye ta wayar salula, yayin da masu shirya fina-finai ke neman sabbin hanyoyin samun masu kallo a zamanin TikTok.

Rahoton Reuters ya bayyana cewa wannan salo, wanda ake kira ‘microdramas’, ya ƙunshi jerin shirye-shirye masu gajeren lokaci, inda kowane sashe zai iya ɗaukar tsakanin daƙiƙa 45 zuwa mintuna biyu. Asalin wannan salo ya samo asali ne daga Chana, amma yanzu ya samu babbar tagomashi a Amurka.

Waɗannan shirye-shiryen suna amfani da labarai masu saurin tafiya, rikice-rikicen soyayya da sauran abubuwan da ke jan hankali cikin ƙanƙanin lokaci, domin masu kallo su ci gaba da kallon sashe bayan sashe a wayoyinsu. Wasu kamfanoni sun fara ganin damar da ke cikin wannan kasuwa, musamman saboda kuɗin samar da irin waɗannan shirye-shiryen ya fi na manyan fina-finai da jerin shirye-shiryen talabijin sauƙi.

Reuters ta ce ana hasashen kasuwar ‘microdramas’ a Amurka za ta samar da kusan dala biliyan biyu a shekarar 2027, yayin da wasu kamfanoni da sabbin dandamali suka fara saka hannun jari wajen samar da irin waɗannan shirye-shiryen.

Wasu manyan kamfanonin Hollywood ma sun fara gwada wannan salo, yayin da fasahar AI ke ƙara sauƙaƙa wasu matakan samar da gajerun bidiyoyin. Haka kuma kafafen sada zumunta kamar TikTok suna zama wata babbar ƙofar da masu kallo ke gano irin waɗannan shirye-shiryen.

Sabon salo na ‘microdramas’ ya kuma buɗe wasu sabbin damar aiki ga masu rubutun fina-finai, daraktoci da sauran ma’aikatan masana’antar nishaɗi da ke neman shiga wata sabuwar kasuwa a daidai lokacin da Hollywood ke fuskantar sauye-sauye masu yawa.

By ukarofi

Leave a Reply