Ƙungiyar kansilolin APC ta taya Yari da Ganduje murnar samun shugabanci a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Kansilolin Jam’iyyar APC ta Ƙasa (NPSCF) ta fitar da saƙonta na taya murnar ga Sanata Abdulaziz Yari Abubakar kuma Gwamnan Jihar Zamfara bisa naɗa shi a matsayin darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta na ƙasa, Hon. Muslihu Yusuf Ali da ya fita a Abuja, ranar Asabar, NPSCF ta kuma taya wanda ta naɗa a matsayin Uban Ƙungiya, tsohon shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje murna bisa samun muƙamin daraktan haɗa kan masu ruwa da tsaki a kwamitin.

A cewarta, waɗannan naɗe-naɗe sahaida ce akan yarda da jajircewa da ƙwarewar jagororin biyu da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban jam’iyyar a matakan jihohi da ƙasa, waɗanda ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen kai ta ga nasara a zaɓen 2027.

Sanata Yari a matsayinsa na mai ƙoƙarin haɗa kan jama’a kuma Marafan Sakkwato hakan ya sa ake masa fatan cimma nasarori yayin zaɓukan. Haka shi ma Ganduje, wanda ƙwarewarsa ta fuskar gudanar da jam’iyya da dabarun zaɓe ta sa ake ganin ya cancanci ya jagoranci harkar samar da goyon baya ga APC a 2027.

Ƙungiyar, a madadin dukkan kansilolin da ke ƙarƙashinta, ta ce tana farin ciki da jagorancin kwamitin da kuma fatan cimma burin samun ƙuri’a miliyan 15 a zaɓen wajen rawar da tsare-tsare, masu ruwa da tsaki da ƙananan hukumomi za su taka don tabbatar da haka.

A ƙarshe, NPSCF ta jaddada goyon bayanta ga tsare-tsaren ƙananan hukumomi 774 domin yin aiki a ƙarƙashin jagorancin Yari da Ganduje wajen tabbatar da gagarumin aikin wayar da kan masu zaɓe, rajista, karɓar katin ɗan ƙasa da kuma uwa-uba ruwan ƙuri’u ga sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a 2027.

By Babaji

Leave a Reply