A daidai lokacin da matsalar yunwa da ƙarancin abinci ke ƙara addabar miliyoyin ’yan Nijeriya, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake fito da wani sabon shiri da take ganin zai taimaka wajen magance matsalar tamowa da rashin wadataccen abinci a ƙasar nan.
Wannan mataki ya zo ne bayan Majalisar ƙasa Kan Samar da Abinci Mai Gina Jiki ta amince da sabuwar Dokar Manufofin Abinci da Gina Jiki ta ƙasa (2026–2035), wadda ake sa ran za ta zama tubalin da za a dogara da shi wajen bunƙasa wadatar abinci da inganta lafiyar al’umma a Nijeriya.
A zahiri, wannan mataki ya nuna cewa gwamnatin Tinubu ta fahimci cewa matsalar yunwa ba wai kawai matsalar tattalin arziki ba ce, illa wata babbar barazana ce ga zaman lafiya, ci gaban al’umma da makomar ƙasa baki ɗaya. Duk wata ƙasa da ta kasa ciyar da al’ummarta yadda ya kamata, tana cikin haɗarin durƙushewa ta fuskar ci gaba da zaman lafiya.
Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana sabuwar manufar a matsayin mafi muhimmiyar doka kan abinci da gina jiki da Nijeriya ta taɓa samarwa.
Kalaman nasa sun nuna cewa gwamnati ta fahimci cewa lokaci ya yi da za a daina tattaunawa kawai, a fara aiwatar da tsare-tsare masu amfani kai tsaye ga talakawa.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda gwamnatin ta umurci dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja su kafa Majalisun Samar Mai Gina Jiki cikin watanni uku kacal. Wannan ya nuna cewa gwamnati na son a samu cikakken haɗin kai daga matakin tarayya har zuwa ƙananan hukumomi domin cimma burin rage yunwa da tamowa.
A ra’ayinmu, wannan tsari ya dace matuƙa, domin matsalar tamowa ta fi addabar yankunan karkara, inda galibin yara da mata ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki. Don haka idan har gwamnati na son ganin wannan manufa ta yi nasara, dole ne ta tabbatar da cewa tallafi da shirye-shiryen sun kai ga talakan da ke ƙauye, ba wai su tsaya a ofisoshi da tarurrukan gwamnati kawai ba.
Haka kuma, gwamnatin ta nuna aniyarta ta tabbatar da ɗorewar wannan shiri ta hanyar ƙirƙiro dokar ƙasa kan abinci da gina jiki, wadda za ta fayyace nauyin da ke kan gwamnatin tarayya da jihohi, tare da tabbatar da samar da kuɗaɗen gudanar da shirye-shiryen.
Wannan mataki abin yabawa ne, domin yawancin kyawawan manufofi a Nijeriya suna mutuwa ne saboda rashin dokar da za ta tilasta aiwatar da su ko kuma rashin kuɗaɗen gudanarwa. Idan aka samu cikakkiyar doka mai ƙarfi, za ta taimaka wajen tabbatar da cewa gwamnatocin gaba ba su yi watsi da shirin ba.
Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa burinsa shi ne ganin babu wani ɗan Nijeriya da zai kwana da yunwa. Wannan buri ya dace da halin da ƙasar nan ke ciki, musamman ganin yadda hauhawar farashin kayan abinci ta jefa talakawa cikin matsin rayuwa.
Sai dai duk da kyawawan manufofin gwamnati, akwai buƙatar a fahimci cewa ba za a cimma nasara da kalamai kawai ba. Akwai buƙatar gaskiya, riƙon amana da cikakken sa ido wajen aiwatar da shirin. Haka kuma, dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware domin wannan aiki sun kai inda ya kamata ba tare da almundahana ko karkatar da su ba.
Bugu da ƙari, gwamnati na buƙatar ƙarfafa harkokin noma, tallafa wa manoma, samar da tsaro a yankunan karkara da rage tsadar kayayyakin noma. Domin babu yadda za a magance yunwa idan manoma na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da matsalolin tsadar taki da iri.
A ƙarshe, wannan sabuwar manufa ta gwamnati na da matuƙar muhimmanci ga makomar Nijeriya. Amma nasararta za ta ta’allaƙa ne kan yadda gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki za su aiwatar da ita cikin gaskiya da jajircewa. ’Yan Nijeriya na jiran ganin sakamako a zahiri — ba kawai alƙawura da manufofi a takarda ba.
