Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta zama ƙasa ta farko a yankin Larabawa da ta haramta wa yara masu ƙasa da shekaru 15 buɗe ko amfani da asusun kafofin sada zumunta, ko da kuwa da izinin iyayensu ne.
Sabuwar dokar, wadda majalisar ministocin ƙasar ta amince da ita, na daga cikin matakan da ƙasashe ke ɗauka domin kare yara daga illolin kafofin sada zumunta kamar fallasa su ga abubuwan da ba su dace ba, yaudarar yara ta yanar gizo, yawan shafe lokaci a gaban allo da kuma amfani da bayanansu ba tare da izini ba.
A ƙarƙashin dokar, an hana yara masu ƙasa da shekaru 15 ƙirƙira, amfani ko gudanar da asusun kansu a shafukan sada zumunta. Haka kuma ba za su iya yin mu’amala da sauran masu amfani, wallafa saƙonni, yin sharhi, raba bayanai ko shiga ƙungiyoyi da tashoshin tattaunawa na jama’a ba.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, WAM, ya ruwaito cewa dokar ta tanadi shekaru 15 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da mutum zai iya amfani da kafofin sada zumunta.
Sanarwar ta ce: “An ƙayyade shekaru 15 a matsayin mafi ƙarancin shekarun amfani da kafofin sada zumunta. Duk wanda bai kai wannan shekarun ba an haramta masa ƙirƙira, amfani ko gudanar da asusun kansa a waɗannan dandamali.”
Sabuwar dokar ta ɗora alhakin tabbatar da bin ƙa’idar kai tsaye a kan kamfanonin da ke gudanar da kafofin sada zumunta, sabanin wasu ƙasashe da ke bai wa yara damar amfani da irin waɗannan shafuka idan iyayensu sun ba su izini.
Sai dai matasa masu shekaru 15 da 16 za su iya amfani da kafofin sada zumunta ƙarƙashin tsauraran matakan kariya. Waɗannan matakai sun haɗa da tace abubuwan da suka dace da shekarunsu, hana mutane baƙi tuntuɓar su cikin sauƙi, kayyade lokacin amfani da na’urori da kuma ba iyaye damar sanya ido kan ayyukansu.
Matakin da UAE ta ɗauka ya sanya ta cikin jerin ƙasashen da ke ƙoƙarin ƙara kariya ga yara a yanar gizo, tare da ƙasashe irin su Australia da Birtaniya waɗanda suma suka fara aiwatar da irin waɗannan dokoki.
Masana na ganin cewa sabuwar dokar za ta taimaka wajen rage illolin da yara ke fuskanta a kafafen sada zumunta tare da ƙarfafa kariyar lafiyar tunani da tarbiyyarsu a zamanin fasahar sadarwa.
