Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya yi iƙirarin cewa an saka sunayen aƙalla sanatoci uku a cikin rahoton da ya ba da shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba tare da sun amince da hakan ba.
Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga kalaman Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, wanda ya bayyana dakatarwar Natasha ta tsawon watanni shida a matsayin ɗaya daga cikin lokutan da suka fi janyo ce-ce-ku-ce a Majalisar Dattawa ta 10.
Da aka tambaye shi ko ya amince da wannan ra’ayi, Oshiomhole ya ce ya yi daidai, yana mai nuni da ƙorafe-ƙorafen da wasu sanatoci suka yi game da yadda aka saka sunayensu a rahoton da ya kai ga dakatar da Natasha.
“Eh, na yarda. Domin akwai wasu da suka ce an saka sunayensu a rahoton alhali ba su sa hannu ba. Misali Sanata Ireti Kingibe ta gaya min cewa ba ta sa hannu a rahoton ba, amma sai ta ga an wallafa sunanta a ciki,” inji Oshiomhole.
Lokacin da aka tambaye shi ko rahoton dakatar da Natasha yake magana a kai, ya tabbatar da cewa shi ne.
“Eh, rahoton da aka gabatar a gaban Majalisar Dattawa kenan,” ya ƙara da cewa.
Oshiomhole ya bayyana cewa tsarin aiki na Majalisar Dattawa ya tanadi cewa kwamitoci su gudanar da bincike tare da sauraron masu ruwa da tsaki kafin su fitar da rahoto da shawarwari.
A cewarsa, bayan kammala aiki, mambobin kwamitin ne ake sa ran su sanya hannu a rahoton domin ya zama matsaya ta bai daya ta kwamitin.
“Idan wani mamba bai amince da abin da rahoton ya kunsa ba, yana da damar kin sanya hannu. Domin sanya hannu yana nufin ka amince da duk abin da ke cikin rahoton,” inji shi.
Ya ƙara da cewa wasu sanatoci guda daya, biyu ko uku sun bayyana cewa ba su sanya hannu ba, amma duk da haka aka saka sunayensu a matsayin waɗanda suka amince da rahoton.
Sai dai Oshiomhole bai zargi wani kai tsaye da yin sa hannu na bogi ba. Ya ce akwai yiwuwar an hada takardar halartar taro da rahoton maimakon sahihan sa hannun mambobin kwamitin.
“Wasu sun ce watakila an hada takardar halartar taro ne da rahoton, wanda bai dace ba. Amma ba ni ne zan yi hukunci a kan hakan ba. Idan Opeyemi Bamidele ya yi irin wannan magana, ya kamata a ɗauke ta da muhimmanci,” ya ce.
Wannan batu na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Sanata Bamidele ya bayyana dakatar da Natasha a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da ƙura a tarihin Majalisar Dattawa ta 10.
A cewarsa, dakatarwar ba ta kasance abin farin ciki ba, domin ta haifar da fahimtar cewa majalisar ba ta da cikakken haɗin kai kuma ba ta ba mata isasshen kulawa.
Duk da haka, Bamidele ya ce Majalisar Dattawa ta samu nasarori masu yawa a fannin dokoki da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen daidaita tattalin arziki da bunƙasa ci gaban ƙasa.
An dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a watan Maris na shekarar 2025 bayan wata taƙaddama da ta barke a zauren majalisa kan tsarin zama.
Bayan rahoton Kwamitin ɗa’a, da ƙorafe-ƙorafen Jama’a, Majalisar Dattawa ta amince da dakatar da ita na tsawon watanni shida.
Hukuncin ya haɗa da rufe ofishinta, dakatar da albashi da alawus-alawus ɗinta, janye jami’an tsaronta da kuma dakatar da wasu gata da ma’aikatanta ke samu.
Natasha ta koma bakin aikinta a watan Satumban 2025 bayan kammala wa’adin dakatarwar, lamarin da ya jawo suka daga ƙungiyoyin farar hula, masana shari’a da wasu daga cikin masu kaɗa mata ƙuri’a, waɗanda suka yi zargin cewa hukuncin ya yi tsauri fiye da kima.
